✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wa’adin Hukumar Katin dan kasa na 2019 ba mai yiwuwa ba ne

A zamanta na mako-mako a ranar Laraba 12 ga Satumban bana,Majalisar Zartarwa ta kasa ta amince da wajabta amfani da Lambar  Shaidar dan kasa  [NIN]…

A zamanta na mako-mako a ranar Laraba 12 ga Satumban bana,Majalisar Zartarwa ta kasa ta amince da wajabta amfani da Lambar  Shaidar dan kasa  [NIN] daga ranar 1 ga Janairun 2019. Wannan a cewar Darakta Janar na Hukumar Katin Shaidar dan kasa (NIMC) Injiniya Aliyu Abubakar Aziz, ya biyo bayan amincewar Gwamnatin Tarayya ta yi ne kan gaggauta fara aiwatar da jadawalin wata sabuwar dabara ta sabuwar fasahar zamani don tantance ’yan kasa.

Sabuwar dabarar tantance ’yan kasar ta  kunshi alkinta rajistar ’yan Najeriya da wadanda doka ta ba su izinin zama a kasar a cikin Ma’ajiyar Bayanan ’Yan Najeriya ta kasa (NIDB).

Aziz ya ce, “Amincewar Majalisar Zartarwar da sabuwar fasahar zamanin tantance ’yan kasar za ta ba da damar fara aiki da dokar Hukumar NIMC ta 23 ta shekarar 2007, wadda ta hada da wajabta amfani da Lambar Shaidar dan kasa (NIN) tare da cin tara ko hukunta duk wanda yake ta dokar kamar yadda yake kunshe a karkashin Sashi na 28 na dokar Hukumar NIMC.”

Aziz ya ce, “Ranar da aka kayyade kan fara adana bayanan wadanda suka cancanta don hade su a NIDB ita ce 1 ga Disamban bana. Wannan yana nufin sai bayanan da aka adana zuwa ranar 30 ga Nuwamba, 2018 ne kadai za a iya daidaita su. Kuma sababbin bayanan mutane wajibi ne su dace da dokokin da aka tsara a cikin Tsararriyar Hanyar  Tattara Bayanai ta Najeriya da Jagoran haka da hukumar ta tanada.

Shekaru da dama Najeriya tana ta kokarin gudanar da aikin samar da katin dan kasa. An dai fara shirin ne da Hukumar Rajistar ’Yan kasa (DNCR)’ wadda ta lakume biliyoyin Naira ba tare da wata nasarar kirki ba, idan aka kwatanta da dimbin kudin da aka kashe mata. Duk da haka, babu wani uziri da aka bayar don bayyana dalilin gazawar wannan shiri duk da cewa kasashe da dama ciki har da Indiya wadda take da yawan jama’a biliyan 1 da miliyan 300 ta samu nasarar gudanar da irin wannan aiki da kudi kadan. Kuma ko a Najeriya irin wannan aiki da ke shafar daukar bayanan mutane kamar na rajistar masu zabe da lasisin tukin mota da rajistar layin wayar tarho da na Lambar Ajiya a Banki (BbN) duk an gudanar da su cikin nasara. Wannan ne ya sa yake da wuya a bayyana dalilin gazawar Hukumar NIMC wajen bai wa ’yan Najeriya da suka cancanta lambar shaidar dan kasa ta NIN.

Shugaba kuma Darakta Janar na Hukumar NIMC a watan Afrilu 2018, ya nuna za a yi amfani da lambar shaidar dan kasa ce a wasu harkoki da aka bayyana a Sashi na 27 na dokar NIMC ta 2007, wadanda suka hada da neman fasfo na kasa da kasa da lasisin tukin mota za su zama tilas ne kawai idan hukumar tare da tallafi daga Bankin Duniya sun samar da cibiyar rajista daya ga dukan mutum dubu 50. Ko ba a fada ba, har yanzu ba a san Hukumar NIMC a akasarin yankunan karkarar Najeriya ba.

A watan Yuni 2018 Injiniya Aziz ya bayyana cewa, Hukumar NIMC tana da cibiyoyin yin rajista 900 a kasar nan, hakan na nufin akasarin kananan hukumomin 774 na Najaeriya ba su da fiye da cibiyar rajistar daya.

Har wa yau a watan Yuni 2018 Injiniya Aziz ya fadi a Kano cewa; “Hukumar na bukatar Naira biliyan 150 don ta sanya dukan ’yan Najeriya a cikin shirin katin shaidar zama dan kasa a shekara uku masu zuwa,” hakan yana nufin a kowace shekara ana bukatar Naira biliyan 50. Kuma ya ce mutum miliyan 31 kacal ne daga cikin miliyan 170 da ake sa ran za a yi wa rijistar suka yi. Don haka akwai bukatar a amsa tambayoyi masu zuwa: Idan Hukumar NIMC tana bukatar Naira biliyan 150 don yi dukan ’yan Najeriya katin shaidar zama dan kasa, mene na amfanin ayyana watan Janairu 2019 a matsayin watan karshe? Kuma idan mutum miliyan 31 kacal ne Hukumar NIMC ta yi wa rajistar a sama da shekara goma da kafata, ta yaya zai yiwu ta yi wa sauran miliyan 140 da ’yan cibiyoyin rajista 900 a kasar nan nan da kwana 100 da za a tilasta aiki da lambar shaidar dan kasa ta NIN?

Amsar wadannan tambayoyi za su tabbatar ko kore zargin da ake yi cewa Hukumar NIMC ta bukaci amincewa da watan Janairu, 2019 wa’adin karshe domin ta matsa wa gwamnati ta hanzarta bayar da Naira biliyan 150 da take nema.

Lura da halin da Hukumar NIMC take ciki, wa’adin da ta bayar ba zai yiwu ba. Don haka muna bai wa gwamnati ta yi watsi da wa’adin har sai Hukumar NIMC ta samar da wadatattun cibiyoyin rajistar a kowane bangare na Najeriya, ciki har da kauyukan da suke lunguna. Sai an yi haka ne barazanar hukumar na za ta hukunta wadanda suka karya dokar za ta samu karbuwa.