✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadume: Kotu da daure mai garkuwa da mutane shekara bakwai

Mai Shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin bayan tabbatar masa da laifukansa.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta daure kasurgumin mai garkuwa da mutanen nan, Hamisu Bala wanda aka fi sani da Wadume, shekara bakwai a gidan Dan Kande.

Mai Shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin bayan tabbatar masa da tuhume-tuhume 13 ciki har da mu’amala da haramtattun makamai da kuma tserewa daga gidan yari.

Kotun ta kuma yanke hukuncin cin sarka ta shekaru uku ga wani sifeton ‘yan sanda mai suna Aliyu Dadje na Babban Ofishin ‘yan sanda da ke Karamar Hukumar Ibi a Jihar Taraba, bisa laifin yin cuwa-cuwa da boye wani laifi.

Bayan Wadume da Dadje, sauran wadanda ake tuhuma da su sun hada da Auwalu Bala (Omo Razor), Uba Bala ( Uba Delu), Bashir Waziri (Baba Runs), Zubairu Abdullahi (Basho) da Rayyanu Abdul.

Mai shari’a Nyako ta yanke wa Delu da Abdullahi da Abdul hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari, yayin da ta wanke Omo Razor da Baba Runs, saboda abin da ta kira neman shaida.

Wasu bayanai sun ce Rayyanu Abdul ne ya bai wa Wadume mafaka a gidansa da ke Kano bayan Wadume ya tsere daga hannun ‘yan sanda a Ibi.

Bayan shari’ar ta shafe shekaru uku, Mai shari’a Nyako ta yanke wa Wadume hukunci a kan tuhume-tuhume biyu da 10 daga cikin tuhume-tuhume 13 da aka yi masa tare da wasu mutum shida.

Ana iya tuna cewa, Lauyan Koli kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ne ya gabatar da karar a gaban mai shari’a Binta Nyako kan wasu tuhume-tuhume da suka hada da kisan kai, garkuwa da mutane, ta’addanci da mallakar muggan makamai.

Wannan dai ya biyo kisan wasu jami’an ’yan sanda uku da wasu fararen hula biyu da sojoji suka yi a ranar 6 ga watan Agustan 2019.

Sojoji goma masu mukamai daban-daban da aka tuhuma a shari’ar Wadume sun hada da; Tijjani Balarabe, David Isaiah, Ibrahim Mohammed, Bartholomew Obanye, Mohammed Nura, Okorozie Gideon, Marcus Michael, Nvenaweimoeimi Akpagra, Abdullahi Adamu da Ebele Emmanuel.