✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar 2021

Kashi 30% na daliban sun samu ‘Credit’ biyar da suka hada da darussan Lissafi da Turanci

Hukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin AFirka (WAEC) ta fitar da sakamakon jarabawarta da aka gudanar a 2021 na dalibai masu zaman kansu.

Babban Jami’in WAEC, Patrick Areghan, ne ya sanar da fitar da sakamakon jarabwar da ya ce an tsara ta ne domin rage tsawon lokacin jiran fitowar sakamakon jarabawar dalibai masu neman gurbin karatu a manyan makarantu bayan kammala karatun sakandare don kar lokaci ya kure musu.

“Dalibai 2,195 —wato kashi 30.1% na dalibai 7,289 da suka rubuta jarabwar— sun samu ‘Credit’ ko fiye da hakan a darussa biyar da suka hada da Lissafi da Harshen Turanci,” inji shi.

Ya kara da cewa kashi 40.1% cikin daliban kuma sun sun samu akalla ‘Credit’ biyar, ciki har da daya daga cikin darussan na Ingilishi ko Lissafi.

Ya bayyana cewa sakamakon ya nuna an samu raguwa da kashi 2.12 na wadanda suka samu ‘Credit’ biyar, ciki har da Lissafi da Turanci, idan aka kwatanta da na 2020.