✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WAEC ta rufe cibiyoyin jarabawa a makarantu 61 a Kogi

A shekara biyu da suka gabata satar jarabawa ta ragu daga cibiyoyi 51 zuwa makaranta daya a Jihar Kogi

Hukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta rufe cibiyoyin jarabawanta a makarantu 61 a Jihar Kogi kan laifin magudin jarabawa.

Hannun agogo ya koma baya ne shekara biyu bayan yawan makarantun da WAEC ta rufe cibiyoyin jarabawarsu kan magudin jarabawa ya ragu daga 51 zuwa daya a fadin jihar.

Bayan samun sakon soke cibiyoyin jarabawan makarantun 61 daga WAEC, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Wemi Jones, ya ce ma’aikatarsa, “Za mu hukunta firinsifal din duk makaranun da suka kunyata jiharmu tare da zubar da kimarta.

“Za mu kafa kwamitin bincike don gano laifin kowane firinsifal, ya yaba wa aya zaki, domin zama izina ga na gaba.

“Ba za ta sabu ba, gwamnati ta rika kashe makudan kudade a bangaren ilimi, amma wasu su rika yi mata zagon kasa, suna bata wa jiharmu suna” in ji shi a ranar Juma’a.

Ya bayyana haka ne a garin Kabba, yayin kammala rabon takardun karatun darussan Fizis da Kemistiri ga manyan makarantun sakandare 95 da ke Mazabar Kogi ta Yamma.

Kwamishinan wanda ya ce a ranar Alhamis WAEC ta aike wa ma’aikatarsa takarda, ya ya ce a shekarar 2019 hukumar ta rufe cibiyoyin jarabawanta a makarantu 51 a jihar.

Amma bayan ma’aikatar ta dauki kwararan matakai sai matsalar ta ragu zuwa makaranta daya tal a jarabawar shekarun 2020 da 2021.

Amm ashe da sauran rina a kaba, bayan jarabawar 2022 kuma sai ga shi abin yi tashin gwauron zabo, ya haura na 2019, daga 51 ya kai makarantu 61.