✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

WAEC ta tabbatar da ranar fara jarrabawa a bana

Tsarin da muka tanada yai daidai da kalandar ilimi kuma an yi shi ne tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.

Hukumar shirya jarrabawar kammala karatun sakandire a Yammacin Afirka (WAEC), ta  yi watsi da jita-jitar da ke yaduwa kan rashin tabbacin yiwuwar zana jarrabawar a bana.

Hukumar ta ce za a gudanar da jarrabawar bana daga ranar 16 ga watan Agusta zuwa 30 ga watan Satumban 2021.

Jami’in hulda da al’umma na Hukumar a Najeriya, Mista Demianus G. Ojijeogu ne ya bayyana hakan yayin mayar da martani dangane da rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka yada kan rashin tabbacin zana jarrabawar a tsakanin watan Mayu zuwa Yuni da aka saba.

Mista Demianus ya ce akwai rashin kyakkyawar fahimta da aka yi wa jawaban da jami’in hukumar, Mista Patrick Areghan ya yi a ranar Talata, yayin bayar da sanarwa a kan sakin sakamakon daliban da suka zana jarrabawar daga ranar 15 ga watan Fabrairu zuwa 11 ga watan Maris na bana.

Ojijeogu ya yi bayanin cewa, an sauya lokacin jarrabawar wanda galibi ake yi a tsakanin watan Mayu da Yuni zuwa watan Agusta da Satumba sakamakon dagula al’amura na tsarin karatu da annobar Coronavirus ta yi.

Ya ce, wannan sauyi na da alaka ne da sauye-sauyen da aka samu a kalanda da kuma taswirar karatu a kasar, wanda ya sanya ba za a iya gudanar da jarrabawar ba a watannin da aka saba yi a baya.

Ya kara da cewa, nan ba da jimawa ba Hukumar za ta fitar da jadawalin zana jarrabawar da zai yi daidai da tsarin karatu na makarantun da ke fadin kasar.

“Tsarin da muka tanada yai daidai da kalandar ilimi kuma an yi shi ne tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya,” in ji shi.