✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wahalar da mata ’yan Najeriya ke sha a Saudiyya

’Yan jarida sun bankado yadda wasu mata ’yan Nejeriya 138 da aka yi safarar su zuwa kasar Saudiyya ke cikin mawuyacin hali. Akalla mata ’yan…

’Yan jarida sun bankado yadda wasu mata ’yan Nejeriya 138 da aka yi safarar su zuwa kasar Saudiyya ke cikin mawuyacin hali.

Akalla mata ’yan Najeriya 138 ne Kungiyar ’Yan Jarida ta Duniya Kan Kudun Hijira (JIFORM) suka gano a cikin kangi a Saudiyya, kwanaki kada bayan an ceto wasu matan ’yan Najeriya a cikin irin yanayin daga kasar Lebanon.

“Tun bayan gangaminmu da ya kai ga ceto ‘yan Najeriya mata 30 a Lebanon da sauran wurare, kungiyoyin kasashe ke tuntubar mu muna hada da hukumar yaki da safarar mutane (NAPTIP)”, inji kungiyar.

Shugaban JIFROM Ajibola Abayomi, a cikin wata sanarwa ranar Lahadi ya ce matan su 138 wani kamfani ne mai suna TTCO ya yi safarar su zuwa Saudiyya domin su yi aiki.

Ya ce rahoton kungiyar yaki da safarar mutane da bautar da yara a Afirka (RAIS) ya nuna matan daga jihohin Najeriya daban-daban, iyayen gidansu sun kwace takardun fasfo dinsu.

Da take kira ga gwamnati ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ceto ’yan Najeriyan, JIFROM ta ce yawancin matan na fama da matsananciyar rashin lafiya da ke bukatar kulawa da sauri.

Shugabar RAIS Omotola Fawunmi ta ce ko da yake kungiyarta ta kokarta wajen ganin an duba lafiyar matan a Saudiyya, tana rokon Gwamantin Tarayya ta yi abun da ya dace wajen ceto su.

Daya daga cikin matan da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce ta roki gwamnati ta kawo musu dauki, tana mai cewa yunkurinsu na samun jakadan Najeriya ya ci tura kasancewar ma’aikata masu karbar baki a ofishinsa ba sa fahimtar Turanci.

Matar ta ce an kai ta Saudiyya ne a matsayin za ta koyar da harshen Turancin Ingilishi a makaranta amma da ta isa kasar sai aka mayar da ita ’yar aikin gida ake kuma azabtar da ita.

Kungiyoyin sun yi takaicin yadda ake azabtar da ‘yan Najeriya da ke zuwa kasashen Gabas ta Tsakiya da sunan yin aiki.

“Muna kira ga hukumomin da ke da alhaki su gaggauta daukar matakan dawo da mata ’yan Najeriya da ke cikin wannan hali a fadin Gabas ta Tsakiya.

Sun ce akwai kuma bukatar daukar kwararan matakan wayar da kai da kuma hukunci domin kawar da matsalar ’yan Najeriya masu tafiya cirani kasashen Gabas ta Tsakiya musamman daga Kudu maso Yammacin Najeriya.

A baya JIFROM ta jagoranci yunkurin dawowa da wasu ’yan Najeriya masu aiki a gidaje a kasar Lebanon bayan matan sun fito a cikin wani bidiyo suna rokon a kawo musu dauki daga Najeriya.

’Yan matan sun koka cewa iyayen gidansu na gallaza musu kuma ba a biyan su kudaden aikinsu na tsawon watanni, lamarin da ya sa su tserewa zuwa ofishin jakadancin Najeriya a kasar ta Lebanon.