✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wahalar da muka sha a hannun mutanen da suka yi garkuwa da mu —Daliban Kankara

Mun dauki kwana biyu kafin mu samu mu saka wani abu a bakinmu.

Wasu daga cikin daliban Makarantar Sakandiren Kankara da aka kubutar a ranar Juma’a, sun bayyana irin halin da suka tsinci kansu bayan da masu garkuwar suka yi awon gaba da su.

Wani dalibi da Aminiya ta fara jin ta bakinsa mai suna Aminu Mudassir Bello, ya ce; “An kwashe mu tun ranar Juma’a 11, ga watan Disamba zuwa ranar 17, ga watan Disambar 2020.

“Hakika mun sha wuya a dajin, musanman bakar yunwa da muka sha saboda ba koyaushe muke samu mu ci abinci ba, mun dauki kwana biyu kafin mu samu mu saka wani abu a bakinmu, suna dai bamu dankali.

“Yanzu mun dawo gida kuma ina cikin farin ciki, amma yanzu haka bani da lafiya amma duk da haka ina fatan komawa makaranta don ci gaba da karatuna,” in ji Aminu Bello.

Aminu Mudassir din ya bayyana cewa, da aka kirga su, su 344 ne amma yanzu dukkansu sun dawo gida, babu sauran mutum ko guda daya da suka bari a can.

Mustapha Idris, shi ma daya ne daga cikin daliban, ya kuma bayyana irin hukubar da suka sha yayin da ’yan ta’addar suka yi garkuwa da su.

“Daga lokacin da aka dauke mu, aka tafi da mu mun sha wahala matuka, kuma bamu yi zaton zamu fito a raye ba.

“Lokacin da suka tafi da mu, muna tafiya suna dukanmu, mun yi wurin kwana hudu a hanya muna tafiya a kasa, munyi zaton muna kusa-kusa sai gashi ma wai mun zo ta bayan Zamfara ma, mun yi matukar mamaki yanzu dai gashi Allah yasa mun fito,” in ji shi.

“Inda muke kwanciya babu kyau, kana kwanciya kwari za su yi ta hawanka, saboda a dandagaryar kasa ne wurin, babu wani abun shimfida, muna kwanciya a inda suke hura wuta, wurin baka iya ware tsakanin kasa da toka, ga sanyi mai tsanani.”

“Su kan bamu dankali da kuli, shi ne kawai abincinmu, su kan bamu ruwa amma ba mai kyau ba, dukkan hannuwanmu da kake gani yana cikin datti ne kuma komai za mu ci sai mun hada da dattinnan na hannuwanmu.”

“Wannan bidiyon da kuka ga an haska mu ne kuma suna yi mana maganar Boko Haram, sun yi mana maganar Jiragen da ake turowa a daina turo su ko kuma duk lokacin da aka turo jirgi za su kashe mutum goma daga cikinmu, lokacin da daya daga cikinsu yake fadawa wanda yake bugo musu waya suke magana da shi yake fada masa haka.

“Basu kashe kowa a cikinmu ba, babu kuma wanda ya bata, wanda ya ce mu 520 ne a lokacin ya rude ne, ba daidai ya kirga ba kansa a kulle yake.

“Ranar da suka dauke mu basu bamu abinci ba, kwananmu biyu babu abinci sai dai mu tsinci ’ya’yan itace mu ci, yanzu haka ba cikin kowa ne yake da lafiya ba a nan.

“Muna iya tsinkar ’ya’yan itace a iyaka inda suka ce mu yada zango, shi ne iya rangwamen da za su iya yi mana kuma kodayaushe a cikin gadinmu suke da bindiga suna zagaye da mu.

“Akwai wani da ya nuna zai gudu, yaron nan ya sha matukar wuya a hannunsu saboda da gari ya waye za su rika watsa masa ruwa, dare yana yi kuma a daure shi, ga duka da suka rika yi masa. Kai gaskiya mun sha matukar wahala yadda ya kamata.”

“Yanzu dai Alhamdulillah, yanzu dai Allah yasa mu sadu da iyayenmu lafiya, komai ya yi kyau Alhamdulillah Alhamdulillah mun gode Allah.”

Shi ma wani dalibi dan aji biyar mai suna Abubakar Salisu, ya yi bayaninsa kamar haka,, yana cewa, “wannan tafiya da muka yi wata kaddara ce ta faru da mu a rayuwa wacce duk cikinmu nan babu wanda zai iya mantawa da ita saboda mun sha wahala wajen tafiya.

“Tun farko dai mun yi zatom ’yan bangar makaranta ne, don har mun watse sai suka rika cewa ku dawo -ku dawo.“Sai suka tara mu wuri guda suka ce mana ina ce hanyar fita daga makarantar, sai suka rika bugunmu suna kora mu, haka muka rika tafiya ba takalmi cikin kaya da saman burji da kafafuwanmu har suka kaimu wancan wajen, saman dutse suka kaimu muka kwana, sanyi ba a magana.

“Da Asuba suka buga bindiga, nan muka tashi muka ci gaba da tafiya, muka yi ta tafiya da Asubar nan har ma suka canza mana wuri, sai da muka kwana muna tafiya har muka isa wani waje, sai suka ce to mu tsaya a nan.

“Muna tafiya ana hutawa har sai da gari ya waye, nan ma muka tsaya muka kwanta suna bamu danyen dankali da kuli guda biyu, idan dankalin guda ne sai a raba a baka rabi, su kuma suna cin biredi ko a kawo musu abinci daga wani wurin su ci mu kuma mu ci dankali da kuli,” in ji Abubakar.

Shi ma Imrana Yakubu dan aji biyar ya ce, “Muna shan ruwan wani rafi da suke wanka a ciki kuma su ba shi suke sha ba ruwan leda suke siyowa daga cikin gari, wasunmu sun kwanta rashin lafiya mu muke kula da marasa lafiyar nan, kuma ba kowa yake cin kulin da dankalin ba saboda batawa mutum ciki yake yi, sai dai kadan-kadan.

“Suna mana barazanar muddin muka koma nan sai sun koma sun kara kamo mu, sun ce banda mun ce likitoci muke son zama da tuni sun kashe mu, tuntuni, in ji Imrana.