✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wahalar fetur ta sa an mayar da hutun mako kwana 3 a Sri Lanka

ma'aikatan da kawai lamarin bai shafa ba su ne masu ayyuka na musamman

Gwamnatin Sri Lanka ta amince da karin kwanakin hutun karshen mako zuwa kwana uku har zuwa tsawon wata uku masu zuwa ga galibin ma’aikata, sakamakon matsalar karancin man fetur din da kasar ke fuskanta.

Wani babban Ministan kasar ya ce ranar Juma’a za ta kasance ranar hutu ga yawancin ma’aikatan da ke aiki a ma’aikatun da ba na bukatu ta musamman ba.

Tsarin ba zai shafi ma’aikata a muhimman sassa kamar bangaren kiwon lafiya da makamashi da ilimi da kuma tsaro ba.

Sri Lanka ta shiga fatara a asusun ajiyar kudadenta na waje kuma karancin shigo da mai ya haifar da wahalar mai a cikin kasar.