✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wahalar man fetur ta mamaye birnin Kano

Yunkurin gwamnati ne na son kara farashin mai.

Jama’a sun wayi gari da wahalar samun ababen hawa da suka yi karanci sakamakon wahalar man fetur da ta mamaye garin Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Fasinjoji da dama ranar Litinin sun yi cirko-cirko a kan titunan Birnin Dabo saboda rashin samun ababen hawa wanda da wahalar man fetur ta janyo musamman a kwanaki biyu da suka gabata.

Wakilinmu ya gano cewa, cikin fiye da gidajen sayar da man fetur 50 da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri, shida ne kawai suka bude suke sayar da man.

Ko da ya zanta da wani direban mota mai suna Abdullahi Idris, wanda ke jigilar fasinjoji daga Wudil zuwa Kano, ya ce tun a ranar Asabar din da ta gabata aka fara samun karancin ababen hawa kuma ga fasinjoji a kasa jingim.

Ya kara da cewa ana zargin cewa karancin man alamace da ke nuni da ana son kara kudin zuwa Naira 300 duk lita maimakon naira 165 da  ake sayarwa a halin yanzu.

Wani direba shi ma da ya saba jigilar fasinjoji daga tashar Hotoro zuwa Wudil mai suna Isah Mamman, ya ce karancin man fetur abu ne da hukuma ta shirya.

“Kusan kowace shekara ana samun irin wannan karancin mai a tsakanin watan Nuwamba da Disamba.

“Amma dalilin da hakan ke faruwa ba wani abu bane da ya wuce yunkurin gwamnati na son kara farashin mai ta yadda a karshe ko an kara baza mu yi korafi ba saboda mun sha wahalar nemana man,” inji shi.

Duk wannan na faruwa ne yayin da a bayan nan Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Malam Mele Kolo Kyari, ya ce an yi tanadin sama da lita biliyan 1.7 na man fetur da kuma wasu lita biliyan 2.3 da ke zuwa, ya kuma yi watsi da rade-radin da ake yi na karancin man fetur din.