✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mutane ke neman masu sayen kuri’unsu a zaben Gwamnan Osun

Masu zabe da wakilan jam'iyyu sun rika cinikayyar kuri'u a bainar jama'a

Masu kada kuri’a sun rika neman wanda zai sayi kuri’unsu a bainar jama’a a zaben Gwamnan Jihar Osun.

Wani rahoton hadin gwiwa na rabin yinin zaben da cibiyoyin bincike da kafofin yada labarai da suka yi aikin sanya ido a kan zaben ne ya bayyana haka.

Tallar kuri’u a fili

“Rahotanni sun nuna mutane sun rika fitowa fili suna neman sayar da kuri’unsu.

“Abin da ya rika faruwa ke nan a rumfa ta 02 Mazaba ta 06 a Karamar Hukumar Iwokan da kuma rumfa ta 03, mazaba mai lamba 03 a Karamar Hukumar Ife ta Kudu.

“Haka kuma abin yake a rumfa mai lamba 03 a mazaba ta 07 a Karamar Hukumar Ife ta Arewa,” a cewar rahoton mai dauke da sa hannun Cibiyar Kirkie-kirkire da Ci Gaban Aikin Jarida (CJID) da kuma Cibiyar Nazarin Bincike ta Duniya (ICIR).

Sauran wadanda suka sa hannu kan rahoton su ne kafofin watsa labarai na Premium Times, Daily Trust, Nairametrics da Orient Daily.

Rahoton ya kara da cewa, “An samu cinikin kuri’u ta yadda wakilan jam’iyyu ke ta rubuta sunayen mutanen da suka amince su sayar musu da kuri’unsu a kan wani farashi.

“Irin haka ta faru a rumfa mai lamba 10, mazaba ta 03 a Karamar Hukumar Ife ta Gabas.”

Kawo yanzu an fara tattara sakamakon zaben a matakin kananan hukumomi 30 da ke fadin Jihar Osun.

Zaben gwamnan na ranar Asabar 16 ga watan Yuli, 2022, shi ne irinsa na bakwai a jihar tun bayan komawar Najeriya tafarkin dimokuradiyya a 1999.

Sauran abubuwan da suka wakana da rahoton ya bayyana sun hada da:

Horo da tura masu sanya ido

Tun kafin zaben, Cibiyar kirkire-kirkire da ci gaban aikin jarida (CJID) wadda a baya ake kira Premium Times Centre for Investigative Journalism (PTCIJ) ta kafa cibiyar nazarin zabukan da za ta sanya ido a kai.

A kan haka ne cibiyar ta horar da kuma tura masu sa ido 39 a dukkan kananan hukumomin jihar Osun domin bayar da rahotanni da bayanai kan irin wainar da ake toyawa a zaben.

Isowar kayan zabe

Tun da misalin karfe 7:00 na safe masu sanya idon suka hallara a rumfunan zabe da aka tura su a fadin jihar domin ganin isowar kaya da jami’an zabe da yadda ake tantance masu zabe da yadda ake kirga kuri’a har zuwa lokacin da za a bayyana sakamakon zaben.

Sun bayyana cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta tura jami’ai da kayan aiki zuwa rumfunan zabe a fadin jihar a kan lokaci.

Zuwa karfe 7:30 na safe jami’an INEC sun isa sama da kashi 70 cikin n100 na rumfunan zaben jihar.

Bude rumfunan zabe

Sai dai duk da haka yawancin rumfunan zabe ba su fara aiki da wuri ba.

Zuwa karfe 12 na rana kashi 40 cikin 100 kawai na rumfunan zabe ne suka fara aiki a kan lokaci,  ragowar 58.9 kuma suka fara a makare.

Na’urar tantance masu zabe

An yi amfani da na’urar tantance masu zabe ta BVAS a duk rumfunan zabe da wakilan namu suka ziyarta.

Amma na’urorin sun ba da matsala a wasu rumfunan zabe a kananan hukumomi irin su Egbedore da Iwo da Oke Adan da sauransu.

Akwai kuma rahoton bacewar  sunayen wadansu wadanda suka yi rajistar zabe a BVAS din.

An hana mutanen da hakan ta shafa jefa kuri’a a zaben, duk kuwa da cewa suna da katin zabe na dindindin.

Masu bukata ta musamman

An bi tanadin dokar zabe ta bangaren ba da fifiko wajen yin zabe ga tsofaffi da mata masu juna biyu da marasa lafiya da nakasassu a kananan hukumomin da aka ziyarta.

Sai dai kuma duk da haka, ba a yi musu tanadi da ya kamata ba, musamman ma nakasassu.

A wasu rumfunan zabe nakasassu da masu tafiya da sanduna ba sa iya shiga wurare masu mahimmanci saboda tudu da matakala.

Ya kamata a kara kula da bukatun nakasassu kamar yadda sashe na 25 na dokar zabe na 2022 ya tanada.

Tashin hankali

Haka kuma an hatsaniya a wasu rumfunan zabe sakamakon rashin aikin BVAS da korafe-korafen yadda aka tafiyar da zaben.

Haka kuma ’yam daba sun haddasa tashe-tashen hankula a rumfa ta  002, mazaba ta 07 a karamar hukumar Orolu, d kuma a mazaba ta 05 a karamar hukumar Iwo LGA, inda wasu da ake zargin ’yan daba ne suka yi artabu da jami’an tsaro.

Dokar COVID-19

An samu karancin bin dokokin kariyar cutar COVID-19, da suka hada da a samu takunkumi da kuma bayar da tazara.

A karshe rahoton ya yi jinjina tare da jaddada goyon bayansa ga masu sanya idon da masu zabe da tare da yi wa kowa fatan alheri da ranar zabe lafiya.