✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wainar da ake toyawa a yakin Rasha da Ukraine

Mako guda da mazauna Ukraine suka wayi garin da karar ankararwa saboda hare-haren da sojojin Rasha ke kaiwa a fadin kasar.

A ranar Alhamis din makon jiya ne kasar Rasha ta kaddamar da yakin mamaya ga makwabciyarta kasar Ukraine bisa zargin ta da shirin shiga Kungiyar Tsaro ta NATO da ta Yammacin Turai da Rashar ke ganin abokan gabanta ne.

Abubuwa da dama sun faru kuma suna ci gaba da faruwa a wannan yaki, inda muka rairayo wasu kamar haka:

A ranar Laraba mazauna Ukraine sun wayi garin shekaranjiya da karar ankararwa saboda hare-haren da sojojin Rasha ke kaiwa a fadin kasar.

Ga abubuwan da muka tattaro, daga BBC:

Aƙalla mutum 21 aka kashe tare da raunata 112 yayin luguden wuta a gari na biyu mafi girma a Ukraine, Kharkiv, a cewar Magajin Garin.

Kuma an samu rahotannin kai sababbin hare-hare a birnin, ciki har da wanda ya hari wani ofishin ’yan sandan yanki da wani bangare na Jami’ar Karazin.

 Sojojin lema na Rasha sun sauka a birnin na Kharkiv da zimmar kwace yankin da ke Gabashin kasar kuma suna ci gaba da kwace garuruwa a Kudu, inda Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce dakarunta sun kwace garin Kherson.

An katse harkokin yaɗa labarai a Ukraine sakamakon harin da aka kai kan gidajen talabijin, inda aka kashe mutum biyar da kuma raunata wadansu biyar, kuma sojojin Ukraine sun umarci mazauna garin Sumy da ke Arewa su nemi gidan buya saboda barazanar harbo makamin atilare, inji Gwamnan yankin.

A Amurka kuma, Shugaba Joe Biden ya yi taron manema labarai yana mai bayyana haramta wa jiragen Rasha bi ta sararin samaniyar kasarsa.

Putin ya ba da umarnin dana makaman Nukiliya

Kakakin Fadar Gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov, ya ce umarnin da Shugaba Putin ya bayar a ranar Lahadi ga dakarun kasar cewa kasance cikin shirin amfani da makaman Nukiliya martani ne ga Sakatariyar Harkokin Wajen Birtaniya, Misis Liz Truss.

Mista Peskov ya ce akwai kalaman rashin kamun kai da ba za a lamunta ba da ke fitowa daga bakin wakilan kasashen Turai game da fito-na-fito a tsakanin NATO da Rasha, ciki har da wanda Ministar Birtaniyar ta yi.

Ministan Tsaro na Birtaniya, Ben Wallace, ya ce Birtaniya ta kalli matsayin na Rasha kan makaman kare-dangin, kuma ta lura cewa babu wani sauyi na a-zo-a-gani a kai.

Ya ce Mista Putin, yana son ya nuna karfin Rasha ne, ta hanyar ambato shirin ko-ta-kwana na amfani da makaman Nukiliya.

Tuni Ministan Tsaron Rasha, Shoigu ya bi umarnin Shugaban na sanya dakarun cikin shirin ko-ta-kwana.

Sannan Amurka ta zargi Shugaban Rasha da zafafa tashin hankalin saboda wannan umarni da ya bayar.

Kakakin Fadar Shugaban Amurka, Jen Psaki ta ce sun saba ganin irin wannan mataki daga Shugaban wanda yake kirkirar karya don biyan bukatun kansa.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda ThomasGreenfield ta yi mummunar suka kan matakin wanda ta ce zai dada zafafa rikicin.

Sakataren Kungiyar NATO, Jens Stoltenberg ya bayyana ikrarin Shugaba Putin da rashin hankali ganin abin da ke faruwa yanzu a Ukraine, inda ya ce hakan zai kara jefa duniya cikin rudani.

Ukraine ta yi ikirarin kashe sojojin Rasha 5,000

 Ma’aikar Tsaron Ukraine ta yi ikirarin cewa sama da sojojin Rasha 5,000 suka mutu a cikin kwana hudu da fara gwabza yaki a Ukraine.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook, jami’an Ukraine sun ce sojojinsu sun hallaka sojojin Rasha 5,300 tare da ikirarin tarwatsa tankuna 191 da jirgin yaki 29 da masu saukar ungulu 29 da motoci masu sulke 816.

BBC da ta ruwaito labarin ta ce ba ta tabbatar da ikirarin ba, amma Ma’aikatar Tsaron Birtaniya ta yi amanna cewa dakarun Rasha sun fi shan wahala a farkon yakin.

Ma’aikatar Tsaron Rasha ma ta tabbatar da wannan ikirari a ranar Lahadi cewa ta rasa sojojinta, amma ba ta yi cikakken bayani kan adadinsu ba.

Darajar kuɗin Rasha ta fadi

An soma ganin tasirin takunkuman da Amurka da kasashen Tarayyar Turai suka kakaba wa Rasha.

A ranar Litinin, darajar kudin Rasha na Rubble a kasuwannin Asiya ta faki da kashi uku bisa hudu Farashin danyen mai kuma ya yi sama da kusan kashi hudu cikin 100.

Hukumomi a Tarayyar Turai sun ce wasu kamfanoni mallakar Rasha da suke cikin kasashensu musamman Sberbank wanda mallakar Rasha ne na daf da samun karayar arziki.

Babban Bankin Tarayyar Turai ya ce Sberbank wanda yake Croatia da Sloveniya ya shiga mawuyacin hali saboda yadda jama’a suka yi ta cire kudadensu.

Tuni mutanen Rasha ke bin dogayen layuka saboda fargabar da suke yi cewa katin bankinsu zai daina aiki kuma za a iya kayyade yawan kudin da mutum zai iya cira daga banki.

Putin ya kira kasashen Turai da ‘taron makaryata’

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya caccaki kasashen Turai inda ya kira su da “taron maƙaryata.”

A wata ganawa da Firayi Ministan Rasha, Mikhail Mishustin da wadansu manyan mukarrabansa bayan jerin takunkuman da kasashen EU suka kakaba wa kasarsa saboda mamayar Ukraine, Shugaban ya ce burinsu na nakasa Rasha ba zai cika ba.

Fadar Kremlin ta ruwaito Putin yana cewa “Ni da Mishustin mun tattauna takunkuman da wadannan ‘taron maƙaryatan’ suka kakaba wa kasarmu, za mu rayu da su, kuma burinsu ba zai cika ba.”

Hana jiragen Rasha ratsa kasashen Turai

An tillasta wa jiragen Rasha yin dogon zango ta hanyar ratsawa ta yankin Kaliningrad da ke tekun Baltic yayin da kasashen Tarayyar Turai suka rufe sararin samaniyarsu ga jiragen kasar.

Kaliningrad, sarari ne mai fadin gaske mallakin Rasha, yana da tazarar kilomita 300 daga Yamma, kuma yana tsakanin Baltic da kasashen Lithuania da Poland na Tarayyar Turai Maimakon bin hanya kai-tsaye ta Latvia da Lithuania.

An tilasta wa jiragen Rasha bin Arewa kusa da St. Peterburg da tekun Baltic.

Kanada ce ta fara hanin kafin kasashen Turai da Birtaniya su hana jiragen Rasha ratsa sararin samaniyarsu.

Ita ma Rasha ta haramta wa jirage daga kasashe 36 shiga kasarta da suka kunshi Birtaniya da Jamus da Spain da Italiya da Kanada.

Birtaniya ta kuma haramta wa Aeroflot sauka a cikin kasarta, wanda ya sa Rasha ta mayar da martani da haramta wa jiragen Birtaniya shiga kasarta.

Mutum miliyan daya sun tsere daga Ukraine

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan daya ne suka tsere zuwa makwabtan kasashe, zuwa Litinin da ta gabata, sakamakon mamayar Rasha.

Kakakin Hukumar, Shavia Mantoo, ta shaida wa BBC cewa, “Alkaluman da muke gani na da tayar da hankali, zan iya cewa abin da na samu daga abokan aikina ne kawai, inda yanzu muna ganin rabin miliyan, wadanda suka tsere daga Ukraine zuwa makwabtan kasashe, a cikin kwana biyar da suka gabata kawai.

“Poland ta ce akwai ’yan Ukraine dubu 250, yawancinsu mata da yara da ake duba takardunsu a kan iyaka; kuma yawanci ana barin su su shiga, har ma wadanda ba a tantance takardunsu ba.

“Maƙwabtan Ukraine na bangaren Yamma sun bar iyakokinsu a bude ga ’yan gudun hijirar.”

Kwamishinar Harkokin Cikin Gida ta Tarayyar Turai, Ylba Johansson, ta ce akwai bukatar Tarayyar ta shirya karbar karin wasu miliyoyin ’yan gudun hijirar.

Daliban Najeriya sun yi tafiyar awa 72 don ficewa daga Ukraine

Yayin da mutane da dama ke ci gaba da barin Ukraine saboda barin wutar da Rasha ke yi a wasu yankunan kasar, ’yan Najeriya ma musamman dalibai da karatu ya kai su can na cikin wadanda suke guje wa tashin hankalin.

Daliban Najeriya da dama sun koka kan halin da suka tsinci kansu a rikicin Rasha da Ukraine da irin bakar azabar da suke fuskanta a hanyarsu ta hijira don neman mafaka.

Wadansu daga cikin daliban sun shaida wa BBC bakar wuyar da suka sha kafin su samu mafaka.

Sarhan Mustapha Salim, na cikin wadannan dalibai na Najeriya, ya ce duk da a yanzu ya isa Budapest a kasar Hungary bayan ya taso daga yankin Dnipro na Ukraine, ya fuskanci bakar wuya kafin ya isa.

Ya ce, “Sai da muka shafe sama da awa 72 kafin mu isa Budapest, don mun shafe kwana uku a hanya, amma alhamdulillah ba tafiyar kafa muka yi ba.”

Sarhan, ya ce a kan hanya bai fuskanci matsaloli ba, a Dnipro ne ya fi fuskantar matsala musamman wajen shiga jirgin kasa saboda akwai cinkoson mutane ga shi kuma babu tikiti.

A ranar Alhamis Gwamnatin Najeriya ta fara debo ’yan kasar da suka tsallaka zuwa kasashe makwabta daga Ukraine.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar ta ce ana sa ran rukunin farko na mutanen su fara isowa Najeriya a Alhamis.

Ta kara da cewa zuwa yanzu hukumomi na da adadin ’yan Najeriya da suka shiga kasashen Romania da Hungary da Poland da Slovekia sama da 2000.

’Yan Najeriya sun yi zangazanga kan mamayar Ukraine

Wadansu ’yan Najeriya sun yi zanga-zangar lumana a gaban ofishin Jakadancin Rasha da ke Abuja, domin kira a kawo karshen yakin da ke gudana a tsakanin Rasha da Ukraine.

Kasashe da dama sun nuna damuwa kan mamayar da Rasha ke yi a Ukraine, inda ake samun zanga-zangar neman zaman lafiya a birane daban-daban na duniya.

Masu zanga-zangar sun yi ta sowa tare da fadin “Muna so a samu zaman lafiya a Ukraine,” dauke da kwalaye masu rubuce-rubucen neman Shugaba Putin na Rasha ya dakatar da yakin.

Ba za a amince da mamayar Rasha a Ukraine ba – Erdogan

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine da abin da ba za a amince da shi ba.

Ya ce yana martaba kasar Ukraine, kuma ya ce ba zai juya baya ga kowace daga cikin kasashen biyu ba.

Mista Erdogan, wanda ya kulla sabuwar alaka ta kut-da-kut da Shugaba Putin a ’yan shekarun nan, ya ce zai iya rage yawan zirga-zirgar jiragen ruwan Rasha da ke bi ta ruwan Turkiyya.

Mai Kungiyar Chelsea ya amince ya sulhunta tsakanin Putin da Ukraine

Attajirin nan dan kasar Rasha, Roman Abramobich ya ce ya amince da bukatar Ukraine ta neman goyon bayansa wajen cim ma matsaya kan yaki a Ukraine.

Mai magana da yawun Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea da ke Ingila, ta ce yana kokarin taimakawa tun farko da aka tuntube shi.

Ta ce wannan shigar ta hana Mista Abramobich – na hannun damar Shugaba Vladimir Putin a fiye da shekara 20 – sakat kan halin da ake ciki a Ukraine.

Wani babban dan kasuwar Rasha – Oleg Deripaska – ya fitar da sanarwar da ke kiran a kawo karshen Jari-Hujja a Rasha.

Hakan ya biyo bayan kalamansa a makon jiya, inda ya yi kiran a gaggauta tattaunawa kan zaman lafiya; yayin da wani attajirin Rasha, Mikhail Fridman, ya bukaci a kawo karshen zub da jini.

Ukraine ta nemi shiga Kungiyar Tarayyar Turai a hukamnce

Yayin da ake tsakiyar fafata yaki, kasar Ukraine ta cike takardun neman izinin shiga Kungiyar Tarayyar Turai (EU) a hukumance.

Babban jami’in ofishin Shugaban Ukraine, Andrii Sybih, ya ce tuni Shugaba Volodymyr Zelensky ya rattaba hannu a takardun, kuma yanzu haka an kama hanyar tafiya da su zuwa hedikwatar EU da ke Brussels.

Sai dukkan kasashen da ke cikin kungiyar sun amince da bukatar Ukraine kafin ta zama mamba, sannan hakan na iya daukar shekaru da dama.

Dan Ukraine ya nutsar da jirgin mai gidansa dan Rasha a Spain

Wani dan kasar Ukraine da yake tuka jirgin ruwan alfarma na wani biloniya dan kasar Rasha ya shiga hannun jami’an tsaro a birnin Mallorca na Spain, bayan an zarge shi da yunkurin nutsar da jirgin mai gidansa da kudinsa ya kai Yuro miliyan bakwai (kimanin Naira biliyan uku da rabi), kwanakin kadan bayan Rasha ta kai mamaya ga Ukraine.

Jirgin, mai tsawon kafa 156 mai suna Lady Anastasia, mallakar Aledander Mijeeb ne wani tsohon Shugaban Kamfanin Kera Helikwafta na Rasha.

Ana zargin direban da bude wata kofa inda ruwa ya rika shiga jirgin ya fara nutsewa.

Matukin jirgin ya ce ya yi haka ne saboda mai gidan nasa yana samar da makaman da ake kashe mutanen Ukraine kamar yadda jaridar Ultima Hora ta ruwaito a ranar Lahadi.