✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wainar da ’yan fim suke toyawa a Indiya

Tun a ranar 28 ga Satumba 2014 ne jarumai da furodusoshi da daraktocin fina-finan Hausa da yawansu ya kai 20 suka halarci kwas a kasar…

Tun a ranar 28 ga Satumba 2014 ne jarumai da furodusoshi da daraktocin fina-finan Hausa da yawansu ya kai 20 suka halarci kwas a kasar Indiya a kan al’marin ya shafi aktin da shirya fim da daukarsa da kuma daraktin.

Gwamnatin Tarayya a karkashin shirinta mai suna Project-Act Nollywood da ta kirkiro don bunkasa harkar fim a Najeriya ce ta dauki nauyin kwas din ’yan fim din a Indiya.
Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ce take kula da yadda ake gudanar da kwas din.
’Yan fim din suna samun horon ne a wata makarantar koyar da aikin fim mai suna Asian School of Media Studies da ke yankin Noida a Birnin New Delhi na kasar Indiya.
A cikin ’yan fim din akwai Jamilu Yakasai da Mustapha Musty da Bashir Rijau da Mohammed Bifa da Ibrahim Mandawari da Hamisu Iyantama da Sani Abdullahi da Aliyu Yakasai da Bala Anas Babinlata da kuma Hauwa Maina.
Sauran sun hada da Farida Rahi da Balarabe Tukur da Usman Adamu da Ishak Sidi Ishak da Umar Labaran da Falalu dorayi da Mika’il Bin Hassan (Gidigo) da Aminu Sabo da kuma Ali Nuhu wanda ya je Indiya a ranar Asabar sakamakon wadansu ayyuka da suka sha masa kai.
A yanzu dai kwas din ya yi nisa inda aka shiga mako na uku. ’Yan fim sun ce sun ziyarci wuraren da ake daukar fim a Indiya, sun kuma tattauna da jaruman fina-finan Indiya da kuma furodusoshi don ganin yadda za a bunkasa harkar fina-finan Hausa.
Alhaji Hamisu Lamido Iyantama ya ce akwai bambanci mai girma tsakanin yadda ake kashe kudi wajen yin fim a Indiya da kuma Najeriya.
Ya ce Indiya sukan kashe kudi mai yawan gaske, sannan suna da kasuwa babba domin a kasarsu kawai sukan yi cinikin biliyoyin Naira ban da wanda ake sayarwa a sauran kasashen duniya.
Ya ce farashin da ake biyan jarumai a kasar Indiya ya sha bamban da yadda ake biyan takwarorinsu a kasar nan, domin a cewarsa akan biya jarumi daya kacal kimanin Naira miliyan 19 zuwa 24 a fim daya.
Ya ce sun koyi dabarun shirya fim, musamamn abin da ya shafi rubuta labari da bayar da umarni da yadda ake sarrafa sababbin kyamara me gwaggwaro (Celleloid) da sauran dabarun shirya fim.
Ya ce sun tattauna da manyan daraktocin fina-finan Indiya da suka hada da Ashok Tyagi, babban editan tace fim da harhada shi na wancan lokaci, wanda ya bayar da umarni ga tsofaffin ’yan fim da suka hada da Deeb Anand da marigayi Rajeesh Khanna da Nasuredden Share da sauransu.
Ya ce wannan kwas din zai ba su damar da za su rika yin fina-finai ta hanya mafi kwarewa da kuma dacewa.
Mika’il Bin Hassan (Gidigo) ya ce sun koyi sabbabin dabarun daukar fim da kuma sabbabin dabarun yadda ake sarrafa kyamara don a samu hoto mai inganci.
Hauwa Maina wadda ta wakilci mata ’yan fim ta ce hakan zai taimaka mata musamman yanzu da take so ta fara daraktin da kuma shirya fim dinta da yaren Babur.
Ana sa ran za su dawo a makon farko na watan gobe idan Allah Ya kai mu.