✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Waiwaye: Kwana 100 cif da fara yakin Rasha da Ukraine

Shugaban Ukraine ya ce yanzu kusan daya bisa biyar na kasar shi na hannun Rasha

A ranar 24 ga watan Fabrairun 2022 ce kasar Rasha ta kaddamar da kai hare-harenta a kan kasar Ukraine a yunkurin hana Ukraine din shiga kungiyar kawance tsaro ta NATO, yau [Juma’a] kwana 100 ke nan cif-cif.

Matakin na Rasha dai a wancan lokacin ya jawo Allah-wadai da martani iri-iri daga sassa daban-daban na duniya, musamman ma kasashen Yamma.

Tun da aka fara yakin dai, miliyoyin ’yan kasar ta Ukraine ne suka gudu suka bar kasar don neman mafaka a wasu kasashen, yayin da ita kuma Rasha ke ci gaba da ruwan wuta ta sama da kasa da kuma ta ruwa a kanta.

A cewar Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, akalla mutum miliyan bakwai ne suka gudu suka bar Ukraine, a daidai lokacin da kasashen Yamma ke ci gaba da kakaba wa Rasha jerin takunkumai.

Tuni dai kungiyar NATO ta fadada yawan kasashenta da kasashen Sweden da Finland, duk kuwa da gargadin da Rashar take ci gaba da yi a kan hakan.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya yi ikirarin cewa ya zuwa ranar biyu ga watan Yunin 2022, kusan kaso 20 cikin 100 na kasarsa yanzu na karkashin ikon Rasha.

Yayin da aka cika kwana 100 da kaddamar da yakin, Aminiya ta duba muhimman abubuwan da suka faru tun daga ranar da aka fara yakin.

21 ga watan Fabrairu: Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya umarci dakarunsa su kutsa kai cikin yankunan Luhansk da Donetsk, ya kuma ayyana su a matsayin yankuna masu cin gashin kansu.

22 ga Fabrairu: Majalisar Dokokin Rasha ta amince wa Putin ya yi amfani da karfin soja a kan Ukraine. Matakin ya janyo Amurka ta kakaba wa bankunan Rasha na VEB da PSB takunkumi.

Daga bisani Jamus ta bi sahun Amurka ta hanyar dakatar da yarjejeniyar shimfida bututan iskar gas ta Nord Stream 2.

24 ga Fabrairu: Rasha ta kaddamar da kai hare-hare a kan Ukraine, inda shi ma Shugaba Zelenskyy ya ba da umarnin daukar matakan kare kasar shi.

Amurka ta sake haramta wa bankunan Rasha biyar yin hada-hadar kudade da ita, sannan ta kulle kadarorin hudu daga cikin bankunan da ke kasarta.

25 ga watan Fabrairu: Rasha ta yi watsi da bukatar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ta janye dakarunta daga Ukraine ba tare da wani bata lokaci ba.

27 ga watan Fabrairu: Dakarun Rasha sun kutsa kai biranen Ukraine uku na Kyiv da Kharkiv da kuma Kherson. Majalisar Tarayyar Turai ta haramta wa jiragen Rasha ratsawa ta sararin samaniyarta.

28 ga watan Fabrairu: Tarayyar Turai ta amince da kashe Yuro miliyan 500 don tallafa wa sojojin na Ukraine.

1 ga watan Maris: An hangi wani jerin gwanon motocin yakin Rasha wanda suka kai tsawon kilomita 65, suna dannawa birnin Kyiv.

9 ga watan Maris: Dakarun Rasha sun kai hari ta sama kan wani asibiti da ke birnin Mariupol da ta mamaye.

10 ga watan Maris: Majalisar Dokokin Amurka ta amince da kashe Dala biliyan 13.6 ga Ukraine.

16 ga watan Maris: Daruruwan mutane sun mutu a Ukraine bayan Rasha ta jefa wani bam a gidan kallo a birnin Mariupol, wanda fararen hula ke samun mafaka a cikinsa.

29 ga watan Maris: Wakilan Rasha da na Ukraine sun fara haduwa a karon farko don tattaunawa a birnin Istanbul na Turkiyya.

2 ga watan Afrilu: Dakarun Rasha sun janye daga garin Bucha, inda aka gano gawawarkin mutane a kan tituna.

8 ga watan Afrilu: Tarayyar Turai ta haramta shigar da gawayi da katako da siminti da kifi da kuma takin zamani daga Rasha.

18 ga watan Afrilu: Dakarun sun kwace iko da biranen Luhansk da Donetsk.

21 ga watan Afrilu: Putin ya ayyana yin nasara a birnin Mariupol.

27 ga watan Afrilu: Rasha ta katse tunkuda iskar gas ga kasashen Bulgaria da Poland, saboda sun ki biyan ta da kudin kasarta na Ruble.

4 ga watan Mayu: A karon farko tun fara yakin, dakarun Ukraine sun sami nasarar fatattakar na Rasha zuwa nisan kilomita 40 daga birnin Kharkiv.

12 ga watan Mayu: Finland ta sanar da yunkurinta na neman shiga NATO.

15 Ga watan Mayu: Sweden ita ma ta sanar da neman shiga NATO bayan shafe kusan shekara 20 a matsayin ’yar ba-ruwanmu.

21 ga Mayu: Rasha ta ce ta kammala kwace birnin Mariupol daga Ukraine, bayan sama da sojojin Ukraine din 2,500 sun mika wuya.

23 ga Mayu: Ukraine ta zartar wa sojan Rasha hukuncin daurin rai-da-rai bayan ta zarge shi da aikata laifukan yaki.

25 ga watan Mayu: Zelenskyy ya caccaki Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Henry Kissinger, saboda shawarar Ukraine ta mika wani bangarenta ga Amurka.

30 ga watan Mayu: Shugaban Amurka Joe Biden ya amince ya aike wa Ukraine karin rokoki don kara karfafa dakarunta.

1 ga watan Yuni: Dakarun Rasha sun kwace tsakiyar birnin Severdonetsk da kuma kusan kaso 70 cikin 100 na birnin.

Kazalika, a ranar Jamus ta yi alkawarin aike wa Ukraine da sabbin makamai na zamani.