✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waiwayen abubuwan da suka faru a yajin aikin ASUU na 2022

ASUU ta dauki tsawon wata takwas tana yajin aiki, lamarin da ya kawo koma baya ga ilimi a Najeriya.

A shekarar 2022 da muke bankwana da ita ce Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da Gwamnatin Tarayya suka yi artabu, lamarin da ya sanya kungiyar shiga yajin aikin wata takwas kafin ta janye.

ASUU ta tsunduma yajin aikin a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar, matakin da ya kai ga masu sasanci shiga a tsakani a rikicin bangarorin biyu.

ASUU dai ta amince ta janye yajin aikin ne a babban taronta na Majalisar Zartarwa da ya gudana a Abuja a ranar 14 ga watan Oktoban wannan shekara da muke bankwana da ita, wanda shugabannin rassanta da sauran manyan jami’ai suka halarta.

A lokacin, lauyan kungiyar, Femi Falana, ya ce, “An amince da janye yajin aikin ne a cikin dare, yau da safe ASUU za ta yi taron manema labarai a Abuja ta sanar a hukumance.”

Shi ma wani babban jami’in ASUU da ya halarci taron ya  ce, “Gaskiya ne, mun janye yajin aikin… Nan gaba da safiyar nan Shugaban ASUU na Kasa zai fitar da sanarwa a hukumance,” kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Janye yajin aikin ASUU na zuwa ne wata takwas cif bayan malaman jami’o’in gwamnati a fadin Najeriya sun bi umarnin uwar kungiyar na daina aiki daga ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022.

Da sauran rina a kaba

Shugabannin Kungiyar sun amince su dakatar da yajin aikin ne a taron da suka shafe tsawon dare, domin su yanke shawarar matakin da za su dauka kan umarnin kotu.

A makon da ya gabaci wannan ne Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta umarci kungiyar ta janye yajin aikin da aka shafe wata takwas a ciki.

Dalilin yajin aikin ASUU

Malaman sun shiga yajin aikin ne bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza cika alkawuran da ta yi musu game da biyan hakkokinsu da suke bi bashi da kuma alkawuran da ta yi musu a jarjejeniyar da bangarorin suka rattaba hannu a 2009.

Baya ga bukatun da suka danganci inganta harkokin karatu da bincike a jami’o’in gwamnati, bangarorin biyu na takaddama kan batun tsarin biyan albashi na bai-daya na IPPIS da gwamnati ke biyan ma’aikata.

ASUU ta ce IPPIS na tauye hakkokin mambobinta, don haka dole a bari su ci gaba da tsarin albashi na UTAS da jami’o’i suka fitar wa ma’aikatansu.

Sai dai gwamnati ta ce allambaran, dole lakcarorin, kamar kowane ma’aikacin gwamnati, su koma karbar albashi ta IPPIS.

Kwan-gaba-kwan-baya

An dade ana kai ruwa rana tsakanin bangarorin, har ta kai ga Shugaban Kasa Buhari ya umarci Ministan Ilimi ya shiga batun ya kuma ba shi wa’adin shawo kan lakcarorin; Amma duk da haka tana kasa tana dabo.

Gabanin haka, zaman da kungiyar ta yi ta yi karkashin jagorancin Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya gaza samar da kyakkyawan sakamako.

Hasali ma, lakcarorin sun karyata ikirarin Ngige na biyan wasu bukatunsu, suna masu nuna rashin sakankancewa da alkawuran gwamnati.

Akalla sau biyu ASUU na cewa ta kara wa gwamnati wa’adin da ta dibar wa kanta domin tattaunawa don yanke shawara a kan bukatun masu yajin aikin.

Lakcarori sun shiga tsaka mai wuya

Tun bayan tsunduma yajin aikin, malaman jami’o’i da yawa sun fada cikin tsaka mai wuya bayan tsarin da Gwamnatin Tarayya ta fito da shi na ‘ba aiki ba biyan albashi’.

Wasu daga cikin malaman sun shiga yin wasu sana’o’i, yayin da wasu kuma ta kai su ga rasa samun abin da za su saka a bakin salati.

Malaman da dama sun soki Gwamnatin Tarayya na nuna halin ko in kula da yanayin da suke ciki ko iyalinsu.

Kasuwancin mutane ya durkushe

Mutanen da ke gudanar da kasuwanci a cikin jami’o’in kasar nan, da yawansu sun karye saboda yadda yajin aikin ya dauki tsawon lokaci ana yin sa.

Da dama sun koka sakamakon kasuwancin ya ta’allaka ne ga hada-hadar da ake yi a cikin makarantu.

Masu gudanar da sana’o’i da suka shafi saye da sayarwa na kayan masarufi da abubuwan da suka shafi amfani yau da kullum sun daina gudanar da komai saboda gudun tafka asara.

Yajin aikin ya tilasta da yawansu sauya sana’o’i yayin da wasu kuma suka ci gaba da jiran tsammani har zuwa lokacin da kungiyar ta janye yajin aikin.

Gwamnati ta maka ASUU a gaban kotu

Daga baya dai, bayan lallashi da alkawuran gwamnati sun gaza shawo kan ASUU, gwamnati ta maka kungiyar a Kotun Kwadago, wadda a karon farko ta umarci kungiyar ta koma bakin aiki.

Rashin gwamsuwa da hukuncin ya sa kungiyar garzayawa zuwa Kotun Daukaka Kara ta Tarayya wadda ta tabbatar da hukuncin kotun farko.

Kotun Daukaka Kara ta yanke hukuncin ne bayan shawarar da ta bai wa bangarorin na sasantawa a wajen kotu ya ki amfani.

Ana cikin haka ne Shugaban Majalisar Wakilai ya shiga lamarin, inda cikin ’yan kwanaki zaman ya fara nuna alamar haske.

A yayin da Majalisar ke sauraron bangarorin, ASUU ta kara zargin IPPIS da rashin inganci da kuma tauye hakkokin lakcarori.

Sai dai a yayin zaman, Hukumar Bunkasa Fasahar Zamani ta Kasa (NITDA) ta shaida wa Majalisar cewa ta yi wa UTAS gwajin inganci a akalla sau biyu, kuma tsarin na gazawa.

Ta ce a duk lokacin da ta kammala gwaji takan sanya ASUU ta kara nazari da inganta tsarin, amma idan aka dawo aka yi wanin gwajin, sai ya fadi.

NITDA ta kuma sanar da gano wasu nakasu da gano a tattare da IPPIS.

Yanke Albashi

Bayan janye yajin aikin ASUU a watan Oktoba, ASUU ta sake yin barazanar shiga wani sabon yajin aiki, inda ta yi kira zaman gaggawa na Majalisar Zartarwarta don yanke shawara kan shiga sabon yajin aiki.

ASUU ta kira zaman gaggawan ne sakamakon rabin albashin watan Oktoba da Gwamnatin Tarayya ta biya malaman jami’a bayan sun janye yajin aiki.

Kwamitin zartarwar ASUU ya ce mambobin kungiyar sun fusata da yanke albashin nasu da suke zargin Ministan Kwadago, Chris Ngige ya yi.