✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wajibi ne mu taimaka wa gwamnati wajen samar da tsaro —Sarkin Jama’a

Ya nemi a rika bayyana maboyar bata gari da kuma lura wajen saukar bakin da ba a sani ba.

Mai Martaba Sarkin Jama’a da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II, ya ce wajibi ne ga kowane mai kishin kasa ya taimaka wa gwamnati wajen samar da tsaro.

Ya nemi al’umma da su rika bayyana maboyar bata gari da kuma lura wajen saukar bakin da ba a san ko su waye ba, tare da kai rahoton duk wani bakon lamarin da ba a gane masa ba ga jami’an tsaro.

Sarkin ya yi wannan kiran ne cikin jawabin da ya gabatar a kofar gidansa da ke garin Kafanchan, jim kadan bayan dawowa daga sallar idi kamar yadda aka saba kowace shekara kafin ya shiga gida.

Ya ce, “idan har kowane sashe da bangare na al’umma za su aikata haka, tare da mikewa tsaye wajen yin addu’o’i a dukkan majami’u, sannan gwamnati ta kara matsa kaimi to ba makawa za a shawo kan matsalolin tsaron da duka addabi kasar.”

Sarkin ya yabawa jama’ar musulmi da kiristocin yankin da ke bai wa masarautarsa hadin kai da goyon baya, tare da jinjina wa jami’an tsaron yankin bisa jajircewarsu wajen lura da duk wani kai-komo da ke wakana a masarautar.

Kazalika, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna kan irin ayyukan da take yi a masarautar da suka hada da gyaran titunan cikin garin Kafanchan da sanya wuta a hanyoyi ciki da wajen garin da kuma gyara kananan Asibitoci da Makarantun Firamare da sauran sassan jihar baki daya.