✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wakilin Babban Hafsan Sojin Kasa ya yi bikin Kirsimeti da dakaru a Yobe

Babban Hafsan ya kuma yi alkawarin ci gaba da kyautata wa dakarun.

A ranar Asabar ne Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Faruq Yahaya, ya kai ziyara ga dakarun rundunar tsaro ta ‘Operation Hadin Kai’ da ke yaki da Boko Haram a garin Damaturu na Jihar Yobe don taya su murnar bikin Kirsimeti.

Babban Hafsan, wanda Kwamanda Manjo Janar Suleiman Idris ya wakilta a sakonsa na bikin Kirsimetin ga sojojin, ya yaba wa rundunar bisa ga yadda take gudanar da ayyukanta cikin nasara.

Ya kuma hore su da su ci gaba don ganin an kai ga nasara, musamman wajen yakin da ake yi da ta’addanci.

Laftanar Janar Faruk ya kuma ce kula da jin dadi da walwalarsu shi ne babban abin da suke ba da fifiko a kai, kuma za su ci gaba da ba su hakkokinsu ta kowace fuska.

Ya kuma yabawa Shugaban Kasa kan yadda yake ba su goyon baya wajen yaki da tada kayar baya.