✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wamakko ya dauki nauyin karatun matasa 45 a Jami’ar Ibadan

Tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya dauki nauyin karatun matasa 45 ‘yan asalin jihar Sakkwato a Jami’ar Lead city da ke birnin Ibadan…

Tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya dauki nauyin karatun matasa 45 ‘yan asalin jihar Sakkwato a Jami’ar Lead city da ke birnin Ibadan na jihar Oyo domin karatun digiri na daya.

Sanata Wamakko a lokacin da yake bai wa daliban takardun gurabun karatun da suka samu, ya roke su da su mayar da hankali a wurin karatunsu.

Tsohon Gwamnan ya shawarci matasan a kan kada su yi wani abu da zai kawo wa karatun cikas, kuma kada su yi wasa da wannan damar da Allah ya basu ta sanadiyarsa.

Ya kuma yi kira gare su a kan kada su yi duk wani abu da zai kawar da martabar danginsu da jihar Sakkwato, yana cewa “ilmi shi ne abu mafi kima da za ka bai wa mutum a rayuwa.”

“Makudan kudin da aka kashe na ganin kun samu wannan damar kar ku yi wasa da ita ku zama jakadu nagari.”

“Ku tabbata ba ku shiga cikin kungiyoyi irin na asiri da wasu za su bata tarbiyarku ba, don gudun da na sani a cikin rayuwa” inji Wamakko.

Matasan za su karanci kwasa-kwasan Injiniyanci da Likitanci domin kara bunkasa fannin ilmi a jihar Sakkwato.

Bayan daliban da za su karanci Injiniyanci da Likitanci akwai masu karatun sanin makamar aikin gwamnati da Sadarwa da Kimiya da sanin halayyar dan Adam da sauransu.