✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wan Mama Taraba, Sanata Abubakar, ya rasu

Sanata Abubakar Abdulazeez Ibrahim ya rasu yana da shekara 64.

Tsohon Majalisar Dattawa mai wakiltar mazabar Taraba ta Tsakiya, Sanata Abubakar Abdulazeez Ibrahim, ya rasu.

Sanata Abubakar wanda wa ne ga tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Sanata Aisha Jummai Alhassan, ya rasu ne bayan rashin lafiya a ranar Talata a gidansa da ke Jalingo.

Sanarwar da iyalansa suka fitar ta ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 1.30 na rana a fadar Sarkin Muri, inda aka sallaci Sanata Aisha Jummai Alhassan.

Sanata Abubakar wanda ya yi zango biyu a Majalisar Dattawa daga 1999 zuwa 2007 ya rasu ne yana da shekara 64.