✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda ya kashe Musulmi 51 a New Zealand ya daukaka kara kan hukuncin kotu

Sai dai har yanzu kotun ba ta sa ranar fara sauraron karar ba

Dan ta’addan nan da ya yi kisan gilla a masallacin New Zealand, ya daukaka kara kan hukuncin daurin rai da ran da aka yanke masa.

A shekarar 2019 mutumin ya halaka musulmi 51 a daidai lokacin da suke ibada a wasu masallatai biyu da ke birnin Christchurch na kasar.

Yanzu dai makashin ya ce bai gamsu da hukuncin da kotu ta yanke masa ba, don haka ya daukaka kara.

Wata majiya daga Kotun Daukaka Karar da ke birnin Wellington, ta fada a ranar Talata cewa ba a kai ga tsayar da ranar da za a soma sauraron karar da makashin ya daukaka ba.

A watan Agustan 2020, kotu ta yanke wa Brenton Tarrant hukuncin daurin rai da rai ba tare da neman afuwa ba bayan ta kama shi da laifin kashe mutum 51 da kuma yunkurin kashe wasu 40.

Bayanai sun ce wannan hari, shi ne irinsa mafi munin da ya taba aukuwa a tarihin kasar ta New Zealand.

Munin laifin da Brenton Tarrant ya aikata, ya sa Alkalin da ya yanke masa hukunci cewa, zai tsananta sharudda a kan hukuncin ta yadda har mai laifin ya mutu ba zai iya kubuta ba.