✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wanda ya nemi yin lalata da karuwa da bindiga ya shiga hannu

Ya tursasa mata amincewa da farashin da yake so ya biya ta

Wani matashi da ake zargi da yunkurin yin lalata da wata karuwa da karfi da yaji ta hanyar nuna mata bindiga ya shiga komar ’yan sanda.

Wani matashi da ya yi yunkurin yin lalata da wata karuwa da karfi da yaji ta hanyar nuna mata bindiga ya shiga hannu.

Kakakin ’yan sandan Legas, CSP Olumuyiwa Adejobi ya ce matashin da aka kama a yankin Surulere na jihar ya yi nemi saduwa da karuwar ce a wani otel, inda ya tursasa ta don ta yarda da kudin da zai ba ta, ita kuma ta ki, ta ce kudin sun yi kadan.

Hakan ya sa matashin ya fito da karamar bindigai kirar pistol domin ya tsoratat ta, lamarin da ya sanya ta yink kururuwa har wasu mutaned dake kusa suka kai mata dauki.

“Jami’anmu ne suka kama
shi, binciken da muka yi mun
gano cewa wanda ake zargin
wasu ’yan fashi ne ke ba shi
ajiyar bindigar, an kuma gano alburusan bindigar guda biyar a tare da shi” inji shi.

Olumuyiwa Adejobi ya
kara da cewa, Kwamishinan
’Yan Sandan Legas ya ba
da umarnin tsare wanda
ake zargin domin gudanar
da bincike.

Ya kuma ba da tabbacin kame ’yan fashin da
ke ba shi ajiyar bindigar.