✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda zai gaje ni sai ya fi ni rusau a Kaduna — El-Rufa’i

Gwamnan ya ce 'yan adawa na kiransa da ‘Mai rusau’ don cusa kiyayyarsa ga jama'ar jihar.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce wanda zai gaji kujerarsa zai yi rusau a jihar fiye da shi.

A cewarsa, wasu mutane na kallonsa a matsayin wanda ya fi mayar da hankali wajen rushe gine-gine a jihar, wanda hakan yasa suke fatan karewar mulkinsa.

  1. Ba ni da niyyar tsayawa takarar siyasa — Sanusi II
  2. Sojoji sun ceto daliban FGC Yauri 9 daga hannun masu garkuwa

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wani shiri na musamman da aka watsa a gidajen rediyon Jihar a daren ranar Alhamis, inda ya bayyana cewar gwamnatinsa ta kawo wa jihar ci gaba mara misaltuwa.

El-Rufai, ya ce gwamnatinsa ta gwammace mayar da hankali wajen raya Jihar da ta baiwa mutane kudi da sunan tallafi.

Ya ce, “Lokacin da muka fara aiki akan makarantu sun ce ba mu gina tituna ba, yayin da muka fara gina tituna kuma suka ce ba mu tallafawa jama’a ba. In har bawa mutane kudi shi ne tallafi, to su ci gaba da cin zarafinmu, amma mun san mutanen da muke yi don su za su ji dadi.

“Yanzu zabe na karatowa, don haka suke kirana da ‘Mai rusau’, a tunaninsu wanda zai gaje ni ba zai rusau ba, da yardar Ubangiji sai ya yi rusau fiye da ni,” cewar El-Rufa’i.

Ya ce jama’ar Jihar sun san irin kokarin da gwamnatinsa ke yi, don haka ya bukace su da su ci gaba da addu’a don samun nasarar gwamnatinsa.