✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane amfani sayo Cristiano Ronaldo ya yi wa Man U?

Shin bukatar da ta sanya kungiyar ta sayo dan wasan daga Juventus ta biya.

A karshen kakar wasannin da ta gabata ne kungiyar kwallo kafa ta Manchester United ta yi zawarcin dan wasa Cristiano Ronaldo daga kungiyar Juventus a kan Fam miliyan 15 da zummar kawo gyara a kungiyar a kakar wasannin bana ta 2021/2022.

A bara ne dai shahararren dan kwallon kafar ya bar tsohuwar kungiyarsa ta kwallon kafa ta Juventus da ke kasar Italiya, ya dawo tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United da tunanin zai kawo gyara a cikinta.

Sai dai wasu na ganin dawowarsa kulob din bai yi wani tasiri ba sosai duba da yadda take shan kashi a wasannin da take bugawa.

Na baya-bayan nan dai shi ne wasan da suka sha kashi a hannun Liverpool da ci 4-0 a filin wasa na Anfield a ranar Talata.

Hakazalika sai kara dandana kudarsu suke yi a hannun sauran manya da kananan abokan hamayyasu a Gasar Firimiya ta Ingila.

Rashin katabus din CR7

Dalilin da wasu ke ganin Ronaldo bai yi wani abin a zo a gani ba shi ne a baya lokacin da yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya zura kwallo 451 a cikin wasanni 438 da ya bugawa mata.

Hakan ne kuma ya kai Real Madrid ga lashe kofunan Zakarun Turai har sau hudu a cikin shekara biyar da kuma kofin Laliga har sau biyu.

A Juventus kuwa ma ya zura kwallo sau 101 a raga cikin wasanni 134, tare da taimakon kungiyar wajen lashe gasar Sirie ‘A’ da kofin Italian Super Cup har sau biyu.

Duba da irin kokari da kuma nasarorin da ya samu na lashe gasanni daban-daban a lokacin da yake Real Madrid da Juventus, ya sa wasu suke ganin ba ya taka wata rawar a zo a gani a Man United.

Ga kuma irin kashin da kungiyar ke sha yau da kullum, inda lokuta da dama a kan lallasa ta, duk da Ronaldo na cikin wasannin.

Sai dai kuma masu sharhi a kan al’amuran kwallon kafa na ganin cewa albarkcin kwallayen da Ronaldo ya ci wa Manchester United a bana ba take ce, ba don haka ba da kungiyar za ta iya tsintar kanta a mataki na takwas zuwa 10 ko kasa da haka, duk da cewa a yanzu tana a mataki na shida a kan teburin Gasar Firimiyar 2021/2022.

A kakar wasannin bana dai Cristiano Ronaldo ya ci wa kungiyar kwallaye 15 tare da taimakawa a ci kwallo har sau uku a Gasar Firimiyar Ingila, inda a Gasar Zakarun Turai ya ci mata kwallo shida.

Duba da yanayin da kungiyar ke ciki a halin yanzu ya ya haifar da ce-ce-ku-ce a kan ko Ronaldo ya bar Manchester United ko kuma ya zauna ya ci gaba da taka musu leda.

Cristiano Ronaldo dai yana daya daga cikin manyan ’yan kwallon da suka shahara a duniyar wasannin kwallon kafa.