✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na neman ciyo bashin tiriliyan N11 a 2023

Muhimman alkaluman kasafin 2023, wanda fannin noma ne na 10 a jerin bangarorin da aka ware wa kudade

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisar Dokoki ta Kasa bukatar ciyo bashin Naira tirilan 11.3 a shekarar 2023.

A Daftarin Kasafin 2023 na Naira tiriliyan 20.51 da ya gabatar a ranar Juma’a, wanda shi ne mafi yawa a tarihin Najeriya, Buhari ya ce za a ciyo bashin Naira tiriliyan 11.3 ne domin cike gibin aiwatar da kasafin.

Tun hawanta mulki a 2015, Gwamnatin Shugaban Buhari, tana yin kasafi ne mai gibi, wanda kudaden da gwamnati ke kashewa a shekara suke zarce wadanda take tarawa, sai ta ciyo bashi domin cike gibin da aka samu a kasafi.

Bashin Naira tiliyan 11.3 da Buhari ke shirin ciyowa shi ne mafi girman bashi a tarihin kasar, wadda ake bin ta bashin tiriliyan N42.8, ciki har da tiriliyan N4.2 da ka ciyo don cike gibin da a aka samu a kasafin 2022.

Da yake gabatar wa Majalisa Kudurin Dokar Kasafin 2023 na tiriliyan N20.51, Buhari ya shaida wa taron cewa Gwamnatin Tarayya na hasashen samun kadaden shiga Naira tiriliyan 9.723, don haka sai ta ciyo bashin Naira 11.3 domin cike gibin.

Ya kuma bayyana cewa gibin da aka samu na kashi 4.78% na kasafin, ya zarce kashi 3% da Dokar Kudi ta 2007 ta tanada.

Kasafin 2023

Ya ce an yi kasafin ne bisa hasashen Dala 70 a matsayin farashin gangar danyen mai, da kuma hako gana miliyan 1.69 na albarkatun mai a kullum a 2023.

Kasafin ya sanya farashin canjin Dala a kan N435.57, habakar tattalin arzikin cikin gida da kashi 3.75 cikin 100, sai kuma hauhawar farashin kaya a kan kashi 17.17

Yadda za a kashe kasafin 2023

Buhari ya bayyana cewa daga cikin kasafin 2023 na Naira tiriliyan 20.51 za ka kashe za a biliyan 8.27 wajen biyan basuka.

Ga jerin yadda za a kashe kudin a dunkule:

  1. Ayyukan Yau da Kullum:  Tiriliyan N8.271 (N8,271,882,354,405)
  2. Biyan Basuka: Tariliyan N6.557 (N6,557,597,611,797)
  3. Manyan Ayyuka: Tiriliyan N4.934 (N4,934,352,745,705)
  4. Hukumomin Gwamnati: Biliyan N722.109 (N744,109,468,797).

Ma’aikatu masu kaso mai tsoka

Daftarin kasafin ya kuma nuna bangaren tsaro ne ya fi samu kaso mai tsoka, inda aka ware masa tiriliyan N1.091, Ilimi a matsayi na hudu da biliyan 663.971, sai lafiya biliyan N508.8 a yayin da Ma’akatar Noma ta za a matsayi na 10 da Naira biliyan 85.4.

Jerin ma’aikatu da hukumomi 10 masu kaso mafi tsoka;

  1. Tsaro — Tririliyan N1.1
  2. Albashi — Biliyan N921.1
  3. Harkokin ’Yan Sanda — Biliyan 777.4
  4. Ilimi — Biliyan 663.971
  5. Lafiya — Biliyan N580.8
  6. Harkokin Cikin Gida — Biliyan 277.7
  7. Wasanni da Matasa — Biliyan N187.1
  8. Mashawarci kan Tsaro — Biliyan N166
  9. Harkokin Waje Biliyan — 93.4
  10. Noma da raya karkara – Biliyan —85.4