✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane dalili ne ya sa mata suka daina yin wankan jego?

A baya-bayan nan wankan jego ya fara zama tarihi musamman a cikin birane da kuma tsakanin ’yan boko

Wankan jego wata dadaddiyar al’ada ce a kasar Hausa da matan Hausawa sukan yi bayan haihuwa na kusan kwana arba’in zuwa sittin ta hanyar yin amfani da tafasashshen ruwan da ake dafawa da ganyen wasu itatuwa sanannu a kasar Hausa.

Babban dalilin da ya sa matan Hausawa ke wanka jego shi ne domin samun karfi da kuzari bayan haihuwa da kuma lokacin tsufa. Wasu kuma  suna yi ne kawai domin sun tashi sun tarar ana yi, ba tare da wani dalili ba.

A baya-bayan nan wankan jego ya fara zama tarihi musamman a cikin birane da kuma tsakanin ’yan boko.

Abin tambaya a nan shi ne, wane dalili ne ya sa mata suka daina wankan jego?

  1. Likitancin Zamani:

Bincike ya nuna likitocin zamani na taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen wankan jego.

Mata da yawa sun tabbatar cewa likitoci na hana su tun lokacin da suka samu juna biyu, yayin da suke zuwa awo.

Akan  fahimtar da su irin illar da ke tattare da wankan da tafasshen ruwa ga lafiyarsu.

Wasu likitocin ma sukan alakanta wankan jegon da yawan ciwon zuciya da hawan jini da ke addabar mata musamman masu yawan shekaru.

2. Wahahar da ke cikin wankan:

Mata da yawa sun daina yin wankan jego ne saboda wahalar da suke sha.

Wannan ya fi faruwa a wajen matan da suka yi haihuwar fari.

Galibi idan mace ta yi haihuwar fari akan nemi tsofaffin mata da aka fi sani da ungwozoma su taru a kanta suna yi mata wanka da tafasshen ruwa, wasu ma suna kuka da ihu saboda masifar da ke tattare da wankan.

Wannan ya sa mata da yawa kan guje wa yin wankan sai an tilasta su tun ma a shekarun baya.

3. Ilmi da wayewar zamani:

Yawaitar ilmi da kuma wayewa ya sa mata da dama a yanzu ba sa yin wankan jego.

Mata da yawa sun fahimci cewa wankan jego ba shi da tushe a addini. Hasali ma addini yana hani a kan duk abin da zai cutar da mutum.

Wasu kuma na gani wankan ya zama kauyanci kuma bai dace da zamani ba.

4. Amfani da kafafen sada zumunta na zamani:

Bincike ya nuna cewa akwai masu wayar da kan mata masu juna biyu da jego da yawa a kafafen sadarwa na zamani da ke fada da duk wani abu na al’ada da zai iya cutar da mai jego tare wadanda ke fahimtar da su abin da ya dace su yi da wanda bai dace ba.

Wannan ya yi tasiri kwarai domin mace tana zaune a dakinta za ta iya samun wannan wayewar kan cikin sauki ba tare da ta je ko’ina ba. Wannan ya wayar da kan mata da yawa akan illar wankan jego.

Wani abu da ya sa kafar yin tasiri shi ne tana ilmantarwa a kan duk abubuwan da suka dangaci kula da lafiyar mai jego da abubuwan da ya kamata ta ci da ma yadda za ta kula da jaririnta.

Haka kuma kafafen sada zumunta sun ba da damar alaka tsakanin mutane daga kasheshe daban-daban na duniya wadanda ba sa yin wankan jego.

Alakar matan kasar Hausa da wadannan mutanen ya sa da yawa sun fahimci abubuwa da ake na al’ada kamar wankan jego ba dole ba ne kamar yadda aka dauka a baya.

Wadannan abubuwa na cikin muhimman abubuwan da suka sa mata da dama a kasar Hausa suka daina wankan jego.