✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane dalili ya sa aka yi ‘keyboard’ a hargitse?

Hikimar da ta sa aka yi wadannan abubuwa a ake tunanin shiririta ce.

Akwai abubuwan amfanin yau da kullum da mutane ke amfani da su wadanda yawancin mutane ba su san san dalilin da ya sa aka yi su a yadda suke ba.

Yawanci ba a san cewa akwai dalilin da ya sa aka yi wadannan abubuwa ba, wasu ma tunaninsu kawai rashin kan gado ne, ba su san cewa akwai dalilai kwarara da suka sa aka yi hakan ba.

Kadan daga cikin wadannan abubuw sune kamar haka:

  • Hargitsa keyboard din kwamfuta

A da lokacin da ake amfani da tafireta a matsayin abin rubutu, keyboard din a shirye yake daga A zuwa Z.

Wannan ya sa masu rubutu da shi saurin lakantar  inda kowane harafi yake, don haka sai suka rika yin sauri wajen rubutu fiye da yadda za ta dauka, har ta kai ga tafireta na yawan lalacewa.

Hakan ya sa daga baya aka hargitsa keyboard, aka kuma kirkiro kwamfuta aka yi keyboard dinsa a haka.

Jan layin takarda

Ana sa jan layin ne saboda a yi maganin beraye daga cin takardar, ko da zai ci takardar idan yaga jan layi zai gudu saboda tsoron kar wani abun cutarwa ne. Kuma hakan na taimakawa wajen tsare muhimmin rubutu a jikin takarda.

Gabobin da ke kan ‘earpiece’

Gabobin ne suka raba wayoyin da ke jikin earpiece kuma su ke bawa waya damar gane wane irin earpiece aka sanya a wayar.

Gaba ta farko ce ke dauke da sautin kunnen dama, daya kunnen hagu, dayar kuma shi ne na abin magana.

Matashin kan kujerar mota mai fita

Dalili ya aka matashin kujerar mai shi ne domin ya zama abin daukin gaggawa. Abin Allah Ya kiyaye, idan hadari ya faru kofar mota ta ki budewa, sai mutum ya zare matashin ya yi amfani da karfen ya fasa gilas din motar ya fice.

Komadar kasan kwalba

Wanna kwalmada ita ke saka kwalba daidaita idan an aje ta a kasa ko aka dora ta a kan wani abu.

Har ila yau takan taimaka wajen kara karfin kwalba.