✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane dan wasa ne zai lashe kyautar Ballon d’Or ta bana?

Wannan shi ne karo na 66 da za a gudanar da bikin ba da kyautar.

A yau Litinin za ba da kyautar gwarzon dan wasa mafi kwazo a fannin wasannin kallon kafa na shekarar 2021/2022

A kowace shekara dai a kan zabo gwarzan ‘yan wasa da suka ba wa kungiyoyisu gudummuwa, musamman a wajen lashe kofuna.

Ga dai ‘yan kwallo biyar da ka iya lashe kyautar ta bana:

Karim Benzema (Real Madrid)

Karim Benzema: a kakar wasar da ta gabata dan wasan ya zura kwallo 48 a raga tare da taimakawa har sau 18 a ci.

Hakazalika, dan wasan ya yi nasarar lashe kofin Zakarun Turai, gasar La Liga da kuma kofin UEFA Nations League da na Supercopa de Espana.

Duba da irin rawar da dan wasan ya take a kungiyar Madrid na samun nasarori a kakar wasar da ta gabata ake ganin zai yi wahala dan wasan bai lashe kyautar ba.

Sadio Mane (Liverpool)

Sadio Mane: Dan wasan dan asalin kasar Sanigal, ya samu zura kwallo 33 tare da taimakwa a ci har sau biyar a wasannin da ya buga ga baki daya, kazalika dan wasan ya samu nasarar lashe kofin FA da Carabao Cup kazalika ya ci kofin Nahiyar Afirika.

Ana ganin cewa shi ma dan wasan zai iya lashe wannan kyautar duba da irin kokarin da yayi a kakar wasannin da ta gabata.

Mohamed Salah (Liverpool)

Mohamed Salah:  Dan wasan gaban Kungiyar Liverpool kuma dan asalin kasar Masar, a kakar wasannin bara ya zura kwallo 33 tare da taimakwa a ci 19, ya samu nasarar cin kofin FA  da Carabao Cup a bara, kazalika dan wasan ya taimakawa tawagar Kasarsa ta Masar kaiwa zagayen karshe na cin Kofin Nahiyar Afirika inda suka zo a na biyu bayan Saniga ta yi nasara a kansu.

Robert Lewandowski (Bayern Munich)

Robert Lewandowski: Tsohon dan wasan gaban Bayern Munich, a kakar wasar da ta gabata ya zura kwallo har sau 57 tare da taimakawa a ci sau 12 a wasannin da ya buga a lokacin da yake taka leda a Bayern Munich.

Dan wasan ya samu nasarar cin kofin Bundesliga da kofin DFL-Supercup.

Kylian Mbappe (Paris Saint-Germain)

Kylian Mbappe: Dan wasan gaba na Kungiyar PSG kuma dan asalin kasar Faransa, ya zura kwallo 49 tare da taimakwa a ci kwallo 31 a kakar wasar da ta gabata.

Kazalika, dan wasan ya ci kofin Ligue 1 da kuma na UEFA Nations League.

Sai dai duk da irin nasarorin da dan wasan ya samu, ana tababar cewa ba zai iya lashe kyautar ba duba da Ligue 1 din bai da wani tasiri idan aka hada shi da irin su Laliga da Firimiyar Ingila.

Sauyin da aka samu a kyautar

Za a bayyana gwarzon dan kwallon duniya da za a bai wa kyautar Ballon d’Or ranar Litinin 17 ga watan Oktoba na kakar 2021/22.

Mujallar Frence Football ce ke karrama dan wasan tamaula da ya taka rawar gani da ba kamarsa a fadin duniya.

Wannan shi ne karo na 66 da za a gudanar da bikin, wanda za a yi a Faransa, don fayyace gwarzon dan kwallon kafa na kakar 2021/22.

Tun ranar 12 ga watan Agustan 2022 aka bayyana wadanda ke takara.

A karon farko a tarihin Ballon d’Or za a bayyana gwarzo bisa kwazonsa a kakar tamaula, maimakon shekara daya.

Lionel Messi mai rike da kyautar bara baya cikin ‘yan takara, kuma a karon farko a shekara 17 da ba sunan kyaftin din Argentina.

Tun daga 2008 Messi da Cristiano Ronaldo ke bani in baka wajen lashe kyautar ballon d’Or, in banda 2018 da Luka Modric ya zama zakara.

To sai dai kuma a bana masana na ganin ba wanda ya kamata ya lashe kyautar fiye da dan kwallon tawagar Faransa da Real Madrid, Karim Benzema.