✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane ne sabon shugaban kasar Afghanistan?

Shugabancin kasar Afghanistan ya danganta da irin salon mulkin da Taliban za ta yi

Kwana guda bayan kammala janyewar dakarun Amurka daga Afghanistan, kasashen duniya sun yi kasake suna jira su ji sanarwa game da wanda zai shugabanci kasar.

Da ma dai tun bayan da kasar ta fada hannun kungiyar Taliban ranar 15 ga watan Agusta, mayakanta kuma suka shiga Fadar Shugaban Kasa a Kabul, ake ta hasashe game da wanda zai dare karagar mulkin kasar.

Tun a wancan lokacin an ba da rahoton cewa Shugaban Addini na kungiyar, Haibatullah Akhundzada, ya shiga tattaunawa da sauran shugabanninta don yanke shawara a kan wanda za a dorawa alhakin tafiyar da kasar.

Salon mulki

Sannan kuma rahotanni sun ce kungiyar ta Taliban tana tattaunawa da jami’an tsohuwar gwamnati a kan yiwuwa kafa gwamnatin hadaka don ganin kasashen duniya bas u mayar da Afghanistan din saniyar ware ba.

Sannan akwai hasashen cewa kungiyar ta Taliban za ta aro salon gwamnatin Iran – wadda ke da shugaban kasa da kuma shugaban addini.

Don haka ne ma masu sharhi da dama suka fi hango Mullah Abdul Ghani Baradar, wanda shi ne Jagoran Siyasan a kungiyar, a matsayin shugaban kasar Afghanistan.

Wane ne Mullah Baradar?

Shi dai Mullah Baradar yana cikin mutum biyu da suka kirkiri kungiyar, kuma ya kasance na hannun daman tsohon shugaban Taliban, watau Mullah Omar.

Bayan mayakan Taliban sun karbe iko da kasar Mullah Baradar ya koma gida – shi ne ke jagorantar ofishin harkokin siyasar kungiyar da ke Doha ta kasar Qatar, inda ya kwashe watanni yana tattaunawa da kasar Amurka da nufin wanzar da zaman lafiya a Afghanistan.

A shekarar 2010, jami’an tsaron kasar Pakistan sun kama Mullah Baradar saboda akidarsa da amintakar da ke tsaninsa da Mullah Omar.

Sai dai kuma sun sake shi a shekarar 2018 bayan da mai shiga tsakani don a sasanta na kasar Amurka, Zalmay Khalilzad, ya bukaci a yi hakan a lokacin mulkin Donald Trump.

Ban da gwagwarmayar yakin da Mullah Baradar ya yi, rahotanni sun yi nuni da cewar ya yi yunkurin hawa teburin shawarwari don a sasanta da abokan hamayyarsu musamman a shekarun 2004 da 2009.

Da wannan ne ake ganin cewa shi Mullah Baradar yana iya tabbatar da sasanci da samun goyon bayan duk wadanda za su iya ganin an tabbatar da shi a matsayin shugaban kasa.

An dai haifi Mullah Baradar ne a shekarar 1968 a yankin Uruzgan, kuma a yanzu shi ne na biyu a jerin shugabannin Taliban, inda yake take wa Haibatullah Akhundzada baya.

Baradar ya girma ne a garin Kandahar, inda aka kirkiri kungiyar Taliban.

Mullah Baradar ya taba rike mukamin mataimakin ministan tsaro na kasar Afghanistan a tsawon mulkin shekaru biyar da Taliban ta yi kafin Amurka ta hambare ta shekaru 20 da suka shude.