✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane sakamako ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda zai haifar?

Shin matakin zai sauya salon yaki da ’yan fashin dajin ko kuwa?

A ranar Laraba ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar cewa gwamnatinsa ta ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata hira ta musamman da gidan talabijin na Channels ya yi da shi, inda suka tattauna kan batutuwa da dama.

Tun da farko mutane da dama sun yi shekaru suna kiran Gwamnatin Tarayya da Shugaba Buhari su ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda, duba da irin kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane da suke yi don karbar kudin fansa.

Hare-haren ’yan bindiga, musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda lamain ya fi kamari a jihohin Katsina, Zamfara, Kaduna, Neja, Sakkwato da Kebbi, sun yi sanadiyyar salwantar rayukan dubban mutane.

Bayan daukar lokaci ana kiran shugaban kasar ya ayyana su a matsayin ’yan ta’adda, daga karshe ya amsa kiran, amma me ya sa ya dauki tsawon lokaci kafin yin hakan?

Ko me ya sa Shugaba Buhari sauya ra’ayinsa sannan ya ayyana su a matsayin ’yan ta’adda?

Idan ba a manta ba, a watannin baya kotu ta ba wa Gwamnatin Tarayya umarnin ayyana ’yan fashin dajin a matsayin ’yan ta’adda.

Hakan na zuwa ne bayan fitaccen malamim addinin Musuluncin nan, Dokta Ahmad Abubakar Gumi, wanda tsohon hafsan soja ne, ya ce bai kamata a ayyana su a matsayin ’yan ta’adda ba.

Bayyana ra’ayin nasa ya jawo ce-ce-kuce a tsakanin mutane, inda wasu suke ganin bai dace malamin ya rika goyon bayan wadanda suke zubar da jinin mutane ba gaira, ba dalili ba.

Malamin dai ya sha yin kira ga gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindiga domin dole ce ta sa su daukar makamai don kare kansu daga irin cin zalin da ake musu; wasunsu kuma rashin ilimi ne ya jefa su a halin da suke ciki.

Abin tambaya a nan shi ne, shin ayyanawar da aka yi wa ’yan fashin dajin a matsayin ’yan ta’adda zai sauya salon yaki da su?

Shin zai haifar da wani sakamako na daban wanda ba a taba samu ba a baya?

Ko kuma matakin na da alaka ne da babban zaben 2023 da ke kara karatowa?