✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane tasiri dawowar Cristiano Ronaldo zai yi wa Man-U?

A ranar Asabar da ta gabata ce Cristiano Ronaldo ya fara wasansa na farko bayan dawowarsa kungiyar Manchester United, inda ya fara da kafar dama…

A ranar Asabar da ta gabata ce Cristiano Ronaldo ya fara wasansa na farko bayan dawowarsa kungiyar Manchester United, inda ya fara da kafar dama bayan ya zura kwallo biyu a ragar Newcastle United.

Cr7 fitaccen dan wasa ne da ya dade yana nuna bajinta ta hanyar zura kwallaye da lashe kofuna a duk kungiyoyin da ya buga, wanda hakan ya sa magoya bayan Manchester United din suka shiga murna na dawowar dan wasan.

Sai dai dan wasan na Portugal ya dawo ne a daidai lokacin da Manchester United take rarrafe ba kamar yadda ya bar ta ba a baya, musamman wajen lashe kofuna.

– Yaushe Man U ta lashe kofinta na karshe?

Manchester United ta lashe kofi na karshe ne a shekarar 2017 a zamanin Jose Mourinho, inda ta doke Ajax da ci biyu da daya a wasan karshe na Kofin Europa.

Shekara hudu ke nan yanzu rabon kungiyar da lashe kofi.

Wannan ya sa kocin kungiyar na yanzu Ole Gunnar Solskjaer yake cikin tashin hankali.

– Tasirin da zai yi

Magoya bayan kungiyar suna ganin dawowar Ronaldo zai taimaka musu wajen lashe kofuna da samun nasara a wasanninsu.

Sai dai wasu suna ganin yanzu shekarunsa sun ja, don haka ba dole ba ne ya yi kamar yadda ya yi a baya.

Kocin Manchest United, Solskjaer ya ce a game da kungiyar a bana, “Mun samu matsaloli a baya. Amma kuma mun samu nasarori da yawa. Kasancewar ’yan wasa irinsu David De Gea da Harry Maguire da suka dade a harkar, muna samun karin nuna kwarewa sosai. Sannan mun samu karin Varane da Cristiano Ronaldo.”

Bayaninsa na nuna cewa yanzu yana da ’yan wasa zarata da yake bukata domin samun nasara, sai dai magoya bayan kungiyar suna tunanin shin Ronaldo zai iya daukar nauyin kungiyar a yanzu kamar yadda yake yi a baya.

Shi dai Ronaldo dan wasa ne da tsufa har yanzu ba ta fara nuna shi ba duk kuwa da shekarunsa.

A kakar bara, shi ne wanda ya fi zura kwallo a gasar Seria A ta Italiya.

Shekara 12 ke nan da Ronaldo ya buga wasan Zakarun Turai na karshe a Machester United, inda Barcelona ta doke Man U da ci biyu da nema.

Bayan wannan, Ronaldo ya lashe gasar Zakarun Turai sau hudu a Real Madrid, sannan shi ne ya fi zura kwallo a gasar, amma tun gasar da Man U ta lashe a shekarar 2008 lokacin yana kungiyar, ba ta sake lashe gasar ba.

Baya ga haka, a wasa 10 na Solskjaer ya jagoranci Man U, hudu kawai kungiyar ta lashe, aka doke ta a shida.

Sai dai shi ma Ronaldo bai nuna tagomashi ba sosai a zamansa a kungiyar Juventus ta Italiya.

A Juventus din, duk da ya zura kwallaye da dama kuma ya lashe kofuna da dama, ya gaza taimaka wa kungiyar ta lashe gasar Zakarun Turai, wanda shi ne babban dalilin dauko shi daga Real Madrid.

Ana sa ran dawowar Cr7 zai taimaka wa kungiyar ta kara karfi duba da yadda yake karawa duk kungiyar da ya buga karfi.

Kungiyar yanzu za a iya cewa ta samu tsari mai kyau ganin tana da ’yan wasa irinsu Pogba da Fernandes a tsakiya da Varane da Maguire a baya da kuma Ronaldo din a gaba da sauran ’yan wasan kungiyar.

Akwai kuma batun jefa kwallaye a raga, wanda wannan ne bangaren da Cr7 ya fi kwarewa. Ita ma wannan matsalar za a iya cewa ta kau.

Duba da dama Manchester United na da zaratan ’yan wasa kwararru, zuwan Ronaldo zai kara dinke musu matsalar da suke da ita.

Daga cikin matsalolin da kungiyar take fuskanta akwai rashin shugaba a cikin fili, wanda zai ‘kwaba’ wa ’yan wasan, wanda da zuwan Ronaldo wannan matsalar za a iya cewa ta kau.

Ronaldo dan wasa ne mai daukar hankali, kuma a duk inda yake, hankali na komawa kansa domin ganin abin da zai buga.

Dawowarsa za ta sauya tunani da tursasa wa sauran ’yan wasan kungiyar su kara dagewa.

Shi ma zai dage domin nuna cewa har yanzu akwai sauransa.

Amma ko kungiyar za ta iya lashe kofuna manya irinsu Firimiyar Ingila da ta Zakarun Turai?

Wannan sai zuwa karshen kakar bana domin an ce ai ga fili ga mai doki.