✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani abu sai a kasata Najeriya

A ina ne mai doki yake komawa kutiri? Lallai kam sai dai a kasata Najeriya.

Ya ku Gizagawan Zumunci, ku zo ku taya ni duba wannan bayanin, watau yadda al’amura suke kasancewa a kasata Najeriya.

Ku bi kadin duk wani furuci da zan furta dangane da wannan kasa, Najeriya. Ku yi nazari irin na cin-kwan-makauniya ga wadannan batutuwa.

Da na ce kasata, na san za ku yi tambaya cikin mamaki, cewa me ya sa na ce kasata, ba kasarmu ba? Ni kuwa na ce kasarmu mana, domin kuwa ita kadai ce ta sha bamban da sauran kininta a Nahiyar Afirka da ma sauran sassan duniya gaba daya.

Najeriya, kasar da tana daya daga cikin kasashen bakar fatar Nahiyar Afirka amma sai ta dauki wani irin salo, wanda ya bambanta ta da duk wata kasa da ke sararin Subuhana. Idan ba a kasata ba, yaushe haka ke kasancewa?

Ta yaushe za ki bambanta da ’yan uwanki da danginki? Irin wannan abu sai a kasata, Najeriya.

Idan ba a kasata ba, wacce ke da yawan al’umma fiye da kowace kasar Afirika, wace kasa ce za ta banzatar da al’ummarta haka sasakai, ba tare da inganta musu tattalin arziki da harkar tsaro ba?

Yaushe irin wannan kasa za ta bar kofofinta tinya-binya, ta yadda kowa zai iya shiga kuma ya aikata abin da ya ga dama, ba tare da shayin komai ba?

Mu duba wannan al’amari fa. A yau ba sai gobe ba, kowane jalli-jagar ya bukaci shigowa kasata, kofa a bude take, zai iya shigowa ko ta sama, ko ta kasa ko ta ruwa ko ta mota!

Ba shigowa kadai ba, zai ma iya yo guzurin duk wani alkaba’i ya ga dama, kuma ya sulalo ya aikata abin da yake so.

Kasata ke nan, Najeriya! Lallai kam wani abu sai kasata Najeriya, inda Allah Ya wadata mu da makamashin fetur, amma maimakon ya zama alheri da wadata ga ’yan kasa, sai ya zama tamkar wata annoba.

Kafin ka yi musu ko yarda da wannan batun, bari in warware maka hujjata.

A lokacin da wasu kasashe da ba su da man fetur amma duk da haka sun mallaki ingantattun matatun mai na zamani, inda suke sayo danyen fetur din, suna tacewa kuma suna amfanar da al’ummarsu da shi; sai ga shi a kasata ana gudanar da akasin haka.

Kasarmu da ke da danyen man fetur amma abin takaici, sai mun fitar da shi waje, an tace mana, sannan mu sake sayo shi, mu dawo da shi cikin kasarmu kuma mu saya da dan karen tsada. Wannan kwamacala sai a kasata, Najeriya.

Idan ba a kasata ba Najeriya, yaushe man kananzir zai gagari talaka? Yaushe iskar gas za ta zama sai gidan wane da wane?

Haka kuma yaushe za a ce jiragen sama sun tsaya cik, saboda karancin sinadarin man da ke burka injinansu?

Yaushe za a ce kamfanonin sarrafa kayayyaki sun kasance a rufe saboda tsadar man dizal da bakin mai, wanda da su ne ake murza injinan da ke tafiyar da ayyukan kamfanonin?

Lallai kam irin wannan kidahumancin, sai a kasata Najeriya.

Har ila yau dai, dangane da wannan batu na fetur, abin yana da daure kai sosai, yadda a kasata Najeriya man ya zama mai haddasa talauci ga talakawa maimakon ya zama sanadin wadatar su.

Mu duba fa, ya zuwa yanzu, babu wata hukuma ko wani jami’in gwamnati da zai iya kididdige maka yawan gangunan man da ake hakowa ko kuma ya gaya maka adadin kudin da ake samu a kullum, ko a wata, ko a shekara.

An bar wannan lissafi sasakai, gwamnati na fitar da nata, ’yan baranda da ’yan sumoga na fitar da nasu ta bakar hanya.

Daga karshe dai talakan kasata kawai ake yi wa wa-kaci-ka-tashi. Wannan bahallatsa sai dai a kasata, Najeriya!

Wasu kasashen kuwa da Allah Ya ba su irin wannan arziki na man fetur, ba haka suke ba. Talakawansu suna shaidawa, sun azurta ta fannonin rayuwa daban-daban.

Bari in sake maimaita batuna: Wani abu sai a kasata Najeriya, inda babu doka! Babu doka mana, tunda kowa abin da ya ga dama yake aikatawa!

Mu dubi yadda ake tukin mota da sauran ababen hawa, babu ka’ida, babu bin dokokin tuki, wanda a sanadiyyar haka, kullum ka duba hanyoyinmu, manya da kanana, za ka ga hadurran ababen hawa ba adadi.

Kasata ke nan, inda mutum zai samu lasisin tukin mota cikin kwana daya, ba tare da an gwada ko jaraba kwarewarsa ba. Irin wannan barankasuwa sai a kasata, Najeriya!

Idan ba a kasata ba, inda babu doka da oda, ina za ka ga an daure mutum na tsawon wata shida, bayan an kama shi da laifin satar biliyoyin Naira, saboda shi shafaffe ne da mai amma an daure wani talaka na tsawon shekara uku, kawai don yunwa ta kama shi ya saci tiyoyin shinkafa?

Wannan sai a kasata, inda shari’a ta zama ta kudi. Idan kana da su sai ka falla wa dan sanda mari, ka sha lalai!

Idan kana da kudi sai ka yi kisan kai kuma ka kwana a gidanka sumul-kalau! Idan ba a kasata ba, a wace kasa ce ake yi wa al’amuran ilimi rikon sakainar kashi?

A ina ne ake biyan malamin makaranta abin da bai fi Naira dubu bakwai da dari biyar ba a wata, alhali alawus din wanke suturar Kansila ya dara Naira dubu ashirin? Wannan sai a kasata Najeriya.

Idan ba a kasata Najeriya ba, yaushe shugabanni, musamman na siyasa za su zabi su rika shirga wa talakawansu karya?

Yau su ce kaza, gobe kuma su ce akasin haka, alhali kuma talakawan suna ci gaba da yi musu biyayya? A kasata ce kawai Majalisa za ta kafa doka, Shugaban Kasa ya sanya hannu, amma kuma a shashantar da amfani da ita.

Mu duba batun dokar nan da aka zartar, inda gwamnati ta amince ta biya mafi karancin albashin Naira dubu 30 ga ma’aikatanta.

Ga shi dai an zartar da doka, Shugaban Kasa har ya sanya mata hannu, amma ga shi ana neman warware ta. Shi ne nake kara tambaya, shin idan ba kasata ba, ina ake yin irin wannan tufka da warwara?

Idan ba kasata ba Najeriya, ina ne wutar lantarki za ta gagari al’umma, duk kuwa da irin dimbin dukiyar da Allah Ya wadata ta da ita?

Idan ba Najeriya ba, wace kasa ce za ta yi ta shigo da kayan abinci daga waje, duk kuwa da cewa Allah Ya albarkace ta da yalwar kasar noma mai albarka, sannan kuma ga ruwa cike da tafkuna da gulabe da koguna? Wannan sakarci sai dai a kasata Najeriya.

Idan ba a kasata Najeriya ba, ina ne ake maida gabas yamma, a maida baki ya koma fari, a maida jiya ta koma yau? A ina ne komai yake tafiya a karkace?

A ina ne mai doki yake komawa kutiri? Lallai kam sai dai a kasata Najeriya.

Ya ku Gizagawan Zumunci, sai mu shiga addu’a, domin Allah Ya kawo mana dauki. Ta yadda komai zai daidaita, ta yadda za mu rika aiwatar da al’amura kamar sauran mutane.

Mu ci gaba da addu’a, ta yadda shugabanninmu za su zama adalai, ta yadda za mu shiga sahun nagartattun kasashen duniya, masu tafiyar da al’amura yadda ya kamata.