✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani dan Majalisar Wakilai ya riga mu gidan gaskiya

Dan Majalisar Wakilai da ke wakiltar mazabar tarayya ta Egor/Ikpoba Okha a Jihar Edo, Jude Ise-Idehen, ya riga mu gidan gaskiya. Dan majalisar ya rasu…

Dan Majalisar Wakilai da ke wakiltar mazabar tarayya ta Egor/Ikpoba Okha a Jihar Edo, Jude Ise-Idehen, ya riga mu gidan gaskiya.

Dan majalisar ya rasu ne da ranar Alhamis a Benin, babban birnin jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu ya fitar, ya tabbatar da mutuwar amma kuma ya ce har yanzu majalisar ba ta san musabbabinta ba.

Marigayin ya kasance dan majalisar jihar ta Edo, kafin daga bisani a zabe shi zuwa Majalisar Tarraya a karkashin jam’iyyar PDP.

Ana ganin Idehen, mai shekara 52 wanda ya samu tikitin sake takarar kujerar tarayyar a zabe mai zuwa na 2023, daman yana fama da wani rashin lafiya da ba a bayyana ba.