✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani gini ya sake rugujewa a Legas

Rushewar ginin ta faru kasa da mako guda da faruwar makamancinta a jihar.

Rahotanni daga birnin Iko sun bayyana cewa wani ginin bene mai hawa biyu ya sake rugujewa a Jihar Legas.

Aminiya ta ruwaito cewa an samu rugujewar ginin da dukun-dukun ranar Asabar a kan hanyar Fadar Ago da ke yankin Okota na jihar.

Ya zuwa yanzu babu wani tabbaci kan girman ta’adin da rugujewar ginin ta janyo, sai dai ta faru ne kasa da mako guda da faruwar makamancinta a jihar.

Ana iya tuna cewa a karshen makon jiya ne Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, ta ce wani gini mai hawa uku ya ruguje a birnin Legas, inda ya kashe mutane takwas tare da jikkata wasu 23.

Bayanai sun ce ginin mai hawa uku ya ruguje ne da misalin karfe 9:30 na daren ranar Lahadin makon jiya a yankin Ebute-Metta da ke birnin na Legas.

Shugaban gudanarwar hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA na shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya Ibrahim Farinloye, ya ce jami’ansu sun gano gawarwakin mutane 8, yayin da aka ceto wasu 23 da suka jikkata.

Matsalar rushewar gine-gine ta dade da zama ruwan dare a Najeriya, inda ko a watan Janairu, sai da mutane uku da suka hada da yara biyu suka rasa rayukansu, yayin da aka ceto wasu 18 bayan rugujewar wani coci a Jihar Delta.

A jihar ta Legas kuwa hankula sun tashi gami da karkata kan neman kiyaye ka’idojin gine-gine bayan da wani katafaren gini mai hawa 21 da ake tsaka da ginawa ya ruguje a unguwar Ikoyi cikin watan Nuwamban bara, inda mutane akalla 45 suka mutu.

Kididdigar da wani mai binciken jami’ar Afirka ta Kudu ya bayyana, ta nuna cewar tun daga shekarar 2005, gine-gine akalla 152 ne suka ruguje a Jihar Legas, hadurran da suka lakume rayukan mutane da dama.