✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani jami’i ya kashe kansa bayan ya kasa kashe budurwarsa

An ba da rahotn cewa wani jami’in Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ya kashe kansa bayan da yunkurin da ya…

An ba da rahotn cewa wani jami’in Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ya kashe kansa bayan da yunkurin da ya yi na kashe budurwarsa ya ci tura.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Legas Bala Elkanah ya tabbatar da faruwar lamarin yana cewa da misalin karfe 1 na daren Asabar caji ofis na Morogbo ya samu kiran waya na kar-ta-kwana cewa jami’in mai shekara 47 da haihuwa ya daba wa budurwarsa mai shekara 37 wuka a cinyarta ta dama.

Elkana ya kara da cewa ’yar matar ce ta yi ihun da ya jawo hankalin makwabta.

“Ihun da yarinyar ’yar shekara 13 ta yi ne ya sa makwabta suka ruga wurin da lamarin ya faru.

“Da take bayani [ga ’yan sanda], yarinyar ta ce mamacin ya sake yunkurin caka wa mahaifiyar tata wuka a ka amma ta tsere daga dakin”, inji Elkana.

An dai ba da labarin cewa marigayin ya daba wa cikinsa wukar sau da dama har sai da hanjinsa ya fito, kuma ya mutu nan take.

An jima ana takaddama

An kuma ce shi da matar sun jima suna sa-in-sa ba kakkautawa bayan ya zarge ta da rashin kamun kai.

Matar ta haifi yarinyar da ta yi ihun ne a wani aure da ta yi a baya.

“[Yarinyar] na cikin koshin lafiya”, inji Bala Elkana.

Bincike na farko-farko ya nuna cewa a watan Fabrairu jami’in ya fara zaman daduro da matar, amma daga bisani takaddama ta barke har ta kai ga ba hammata iska a tsakaninsu, inji ’yan sandan.