✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum a Daura ya rataye kansa saboda fatara da yunwa

Ana zargin yunwa da fatara ce suka yi sanadi.

Wani mutum a garin Daura da ke Jihar Katsina ya kashe kan shi ta hanyar rataya saboda tsintar kansa cikin kunci na rayuwa.

Bayanai sun ce mutumin ya debe wa kansa tsammani ne saboda yunwa da fatara ce ake zargi suka yi sanadi.

Aminiya ta samu rahoton cewa, mutumin wanda ba a fadi sunan shi ba, ya dade yana wannan yunkuri na kashe kan shi saboda tsananin talauci da yunwa.

Sai dai kuma wata majiyar ta ce, ana zargin mutumin yana da tabin hankali, domin ya sha fadin zai kashe kan shi.

Zuwa yanzu dai babu wani bayani a hukumance da ya tabbatar da sanadiyar mutuwar mutumin ta hanyar rataya.

Aminiya na ci gaba da bibiyar lamarin a halin yanzu domin samun cikakken rahoto.