✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani ya rasa ransa garin raba rigimar ma’auarata a Imo

Obum rike da wuka ya rarako duk wadanda suka kawo wa matar dauki.

Thompson Onyekuru, wani limamin cocin Redeemed Christian Church of God a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ya rasa ransa a kokarin kubutar da wata matar aure daga ukubar da mijinta ke gana mata.

Rahotanni sun ce Onyekuru ya yi gamo da karshensa ne yayin raba wata rigima da ta yi muni a tsakanin mijin da matarsa da ke zaune a garin Umuokota na Karamar Hukumar Owerri ta Yamma.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ma’aurantan dai sun debo rigimar da ta kai ga mijin ya yanki matar da wuka a wurare daban-daban a jikinta sannan ya kulle ta a daki tare da jaririnta.

Sai dai bayanai sun ce mijin mai suna Obun, wanda dan asalin garin Obowo ne a Jihar Imo, ana zargin yana da tabun hankali.

A cewar shaidun gani da ido, lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na Yammacin ranar Lahadi, yayin da aka jiyo matar Obum mai suna Ogeshi, tana tsala ihu neman a kawo mata agaji tare da jaririnta dan shekara daya kacal.

A kan haka ne Onyekuru da wasu mazauna yankin suka kai dauki domin hana Obum kashe matarsa.

Sai dai a yayin da mutane suka yunkuro domin ceton matar, sai Obum rike da wuka ya yi barazanar kashe duk wanda ya nemi hana shi cimma manufarsa, a cewar wani mai ba da shaida.

Bayan an samu nasarar ceto matar ce sai Obum rike da wuka ya rarako dukkan wadanda suka kawo mata dauki, inda aka yi rashin sa’a ya daba wa Onyekuru wuka a gadon bayansa.

Wasu jami’an ’yan sanda da ke sintiri a yankin sun kai dauki wurin da lamarin ke faruwa, inda a kokarinsu na kama Obum, ya kai wa wani jami’in dan sanda hari.

Hakan ta kai ga sai da jami’an ’yan sanda sun harbe shi a kafa gabanin su iya shawo kansa kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

Nan da nan aka garzaya da ma’auratan da kuma Onyekuru zuwa asibiti, inda duk a can suka ce ga garinku nan.

A yayin da ana isa asibitin ne Onyekuru ya ce ga garinku, an samu tazara tsakanin mutuwar Obum da matarsa, wadanda suka mutu a lokuta daban-daban.

Shugaban yankin, Honarabul Charles Anozie ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba a iya jin ta bakin Jami’in Hulda da Al’umma na rundunar ’yan sandan jihar ba, CSP Mike Abatam.