✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum ya yi wa agolarsa fyade

Ya shaida wa 'yan sanda da suka cafke shi cewa ya lalata karamar yarinyar.

Yan sanda sun kame wani mutum da ya yi wa agolarsa ‘yar shekara 9 fyade a Jihar Adamawa.

Kakakin ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje ya gabatar da mutumin yana mai cewa rundunar jihar ta tashi haikan domin yaki da fyade da cin zarafin kananan yara.

“A ranar 20 ga watan Yuli ne muka kame wani mai shekara a garin Jimeta da laifin yi wa agolarsa Yar shekara 9 fyade.

“Ya amsa laifinsa sannan yarinyar na karbar kulawa a asibitin da ake duba lafiyar yaran da aka yi wa fyade”, inji shi.

Hukumar ta kirayi jama’a da su tashi tsaye domin yaki da fyade da kuma kulawa da yaransu mata kanana.

Nguroje ya kuma bukace su da su ci gaba da tona asirin masu aikata fyade domin a samu nasarar ceto al’umman daga ayyukansu miyagun.