✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani saurayi dan acaba ya mayar da N20m da ya tsinta

Ana kiran shi 'mai kashin tsiya' saboda ya mayar da Dala 50,000 da ya tsinta.

Wani saurayi da ke sana’ar acaba ya zama gwarzo bayan ya tsinci Dala 50,000 (kimanin Naira miliyan 20) a kan hanya ya kuma mayar wa mai su a kasar Laberiya.

Emmanuel Tuloe mai shekara 18 yana tsaka da tuka babur din da yake acaba da shi a kan wani babban titi ne ya tsinci tulin dalolin a nannade a cikin wata jakar leda.

“Na ji tsoro saboda kudaden na da yawa sosai, sai na dawo da su gida na ba wa gwaggona ta ajiye sai an mai su ya yi cigiya,” inji Emmanuel, mazaunin garin Gbolor Dialla da ke kusa da iyakar Laberiya da kasar Kwaddibuwa.

A ranar kuma, “Sai aka ji wata ’yar kasuwa mai suna Musu Yancy ta je gidan rediyo tana kuka tana cigiyar kudinta, tare da rokon duk wanda ya tsinci kudin.”

Daga nan sai Emmanuel ya kai mata, inda hukumar yaki da rashawa ta kasar ta gode mishi bisa nagartar da ya nuna, ’yar kasuwar kuma ta ba shi tukwicin Dala 1,500 (kimanin Naira 615,000) daga cikin kudin.

Ya ce zai raba kutwicin da mutanen da ke tare da shi a lokacin, “Wannan katifar kuma kakata zan ba wa.”

– ‘Mutane na kyama ta’ –

Emmanuel ya ce mutane da dama a kasar na yaba masa, amma wasu, ciki har da abokansa na zulayarsa cewa shi sakarai ne da ya mayar da makuden kudaden da ya tsinta alhali ana cikin matsin talauci a kasar, da ke neman gyagijewa bayan shekaru ana yakin basasa.

“Dun daga lokacin da na mayar da kudin, duk sadda babur dina ya samu matsala a kan hanya, wasu abokaina da abokan sana’a ta ko sun gan ni ba sa taimaka min, saboda suna ganin na  yi wauta da har na tsinci kudi na mayar wa mai su.

“Sai su ce ba zan taba yin arziki ba, tun da na tsinci kudade masu wannan yawa na mayar to a matsiyaci zan rayu har in mutu,” ,” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP.

Ya ce ana yawan yin baranzanar daukar ransa saboda ya mayar da kudin da ya tsinta. “Ina bukatar in kare kaina,” inji shi.

Tuloe ya kuma shawarci matasa da su kasance masu gaskiya da rikon amana, su rika mayar da abubuwan da suka tsinta ga masu su.

“Idan mai kaya ya yi cigiya a mayar mishi, ba wanda ya san gobe,” inji shi.

– Karramawar gwamnati –

Shugaban Kasar Laberiya, George Weah, ya gayyaci Emmanuel domin karrama shi bisa abin da ya yi.

A lokacin da aka aika masa da goron gayyata daga Fadar Shuaban Kasar, matashin, wanda ya bar makaranta tun yana aji daya da sakandare ya koma sana’ar acaba, ya ce, “Idan muka hadu zan yi masa magana a kan yadda za a yi a koma makaranta in ci gaba da karatu.

“Zan kuma bukaci ya ba wa matasa shawara su bar sana’ar acaba su koma makaranta domin sana’ar ba ta da wani riba.”