✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wankan gulbi ya yi ajali dan shekara 10 a Jigawa

Ajali ne ya yi kiran yaron wanda ya tafi wankan rafi tare da abokanansa a kuayen Lelen Kudu.

Rahotanni sun bayyana cewa, wani yaro mai shekaru 10 ya nutse a wani gulbi a Karamar Hukumar Buji da ke Jihar Jigawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Tsaro ta Sibil Difens, CS Adamu Shehu ya fitar ranar Lahadi a Dutse, babban birnin jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, ajali ne ya yi kiran yaron wanda ya tafi wankan rafi tare da abokanansa a kuayen Lelen Kudu a ranar Asabar.

Shehu ya ce an tsamo gawar yaron bayan kusan sa’a biyu da nutsewa, wanda wani likita ya tabbatar da ya riga mu gidan gaskiya.

Mai magana da yawun ya gargadi iyaye da su ja kunnen ’ya’yansu a kan hatsarin da ke tattare da zuwa wankan rafi musamman a wannan lokaci na damina da gulabe da kududdufai suka cika suka tumbatsa.