✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wankan rafi ya yi ajalin dalibi a Ilorin

Ragowar abokan dalibin sun tsere bayan ganin ya nutse a ruwa.

Wani dalibi na karamar Makarantar Sakandare ta Gbagba da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, ya yi gamo da ajalinsa yayin da ya tafi wanka rafi tare da abokansa.

Dalibin, wanda aka ce yana da kimanin shekara 14, ya kasance a rafin tare da wasu abokansa lokacin da lamarin ya faru.

  1. Karin dalibai 3 sun kubuta daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  2. Zuwan Buhari Kano a da, da yanzu

Rahotanni sun bayyana cewa, abokan dalibin da ba a bayyana sunansa ba sun tsere yayin da suka lura yana nutsewa a cikin ruwa.

Wani ganau mai suna Mutiu ya ce, “Mun ga akalla daliban karamar sakandaren Gbagba shida a bakin kogin, sai kuma ba zato ba tsammani muka ji mutane suna ihun a kawo dauki.

“Yayin da muka isa wurin, sai muka gano cewa daya daga cikin daliban ya nutse a cikin ruwan kuma ragowar daliban duk sun tsere.

“Kafin mu iya ceton shi tuni ya riga ya mutu.

“Bayan an tsamo gawarsa, mun ga alamun rauni a kansa wanda ya nuna kamar ya bugu a jikin wani dutse da ke cikin ruwan,” in ji shi.

Da aka tuntubi kakakin Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), Babawale Afolabi, ya ce ba shi da labarin faruwar lamarin, amma ya ce “Zan bibiyi lamarin domin samun karin bayani.”

Har ya zuwa wannan lokacin hada wannan rahoto bai kira ba ko yin wani karin bayani dangane da tabbacin faruwar lamarin.