✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wanne hali ake ciki a Burkina Faso bayan juyin mulki?

Rahotanni sun ce Mutane sun koma harkokinsu na yau da kullum a kasar.

Al’ummar kasar Burkina Faso na ci gaba da gudanar da al’amuransu na yau da kullum kamar yadda suka saba, kwana daya bayan juyin mulkin da ya hambarar da Shugaba Roche Kaboré a kasar.

Da safiyar Litinin ne dai sojoji a kasar suka sanar da tsare Shugaba Kabore bayan sun hambarar da gwamnatinsa.

Bugu da kari, sojojin sun kuma dakatar da Kundin Tsarin Mulkin kasar, sun rusa majalisar dokokin kasar tare da rufe Majalisar Dokokin kasar.

Sun dai zargi hambararren Shugaban da gaza yayyafa ruwa ga wutar rikici a kan iyakokin kasar, lamarin da suka ce ya sa ta’addanci ya dada ta’azzara a cikinta.

Alhaji Muhammadu Kabirou wani dan kasuwa a Oaugadougou, babban birnin kasar, ya shaida ma Aminiya ta waya cewa yanzu mutane na harkokinsu babu wata matsala.

Ya ce akasarin mazauna birnin na nuna farin cikinsu da juyin mulkin sojoji.

“Kowa na jin dadi yanzu mutanen sun taru a wani babban fili na kasar suna jira sojoji su zo su musu marhaba, suna ta wahala.”

Alhaji Muhammadu ya kara cewa sun sha wahala a zamanin mulkin Kabore, yadda aka yi ta kashe-kashen mutane, sannan ’yan gudu hijira sunyi karu matuka.

“’Yan gudun hijira sun yi yawa, mutane sun tarwatse, makaranta duka an kukkulle ko ina. Gaskiya mutane suna neman mafita, sai Allah ya kawo mana sojoji, sunbyi daidai da yadda muke so,” inji shi.

Rahotanni dai sun ya ce al’ummar Burkina Faso sun yi farin ciki da juyin mulkin tare da kyakkyawan fatan samun sauyi a kasar.

Sojojin da suka aiwatar da juyin mulkin dai sun kira kansu da Kungiyar ’Yan Kishin Kasa Masu Kokarin Ceto Kasar.

Laftanar Kanal Paul-Henri Sandogo Damibia ne shugaban wannan kungiya kuma shi ne ya zama sabon Shugaban Kasar.