✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Wasannin da za a fafata ranar Talata a gasar Zakarun Turai

Wasanni takwas za a fafata tsakanin kungiyoyin 16.

A Yammacin Talatar nan za a soma wasannin farko na cikin rukuni a gasar Zakarun Turai ta kakar 2022/2023.

Wasanni takwas za a fafata tsakanin kungiyoyin 16, inda kowacce za ta yi kokarin fitowa kwanta da kwarkwarta tana mai fatan samun nasara.

Wannan ce gasa ta 68 da za a gudanar karo na 31 tun bayan da aka sauya fasalin wasannin.

Real Madrid wacce ita ce kan gaba a bajinta a tarin gasar, ta lashe ta sau 14 kuma ita ce mai rike da kambu a yanzu bayan doke Liverpool da ta yi a fafatawar da suka yi a karkashen kakar da gabata a Faransa.

Yadda kungiyoyin suke a kowane rukuni:

Rukunin A: Ajax, Liverpool, Napoli, Rangers

Rukunin B: Porto, Atletico Madrid, Bayer Leverkusen, Club Bruges

Rukunin C: Bayern Munich, Barcelona, Inter Milan, Viktoria Plzen

Rukunin D: Eintracht Frankfurt, Tottenham, Sporting Lisbon, Marseille

Rukunin E: AC Milan, Chelsea, RB Salzburg, Dinamo Zagreb

Rukunin F: Real Madrid, RB Leipzig, Shakhtar Donetsk, Celtic

Rukunin G: Manchester City, Sevilla, Borussia Dortmund, FC Copenhagen

Rukunin H: Paris St-Germain, Juventus, Benfica, Maccabi Haifa

Wasannin da za a fafata ranar Talata

(Rukunin E)

Dinamo Zageb da Chelsea

Alkali: Istvan Kovacs (Romania)

Wuri: Filin wasa na Stadion Maksimir

Lokaci: 5:30 na Yamma

FC Salzburg da AC Milan

Alkali: Srdjan Jovanovic (Serbia)

Wuri: Red Bull Arena

Lokaci: 8:00 na Yamma

(Rukunin F)

Celtic da Real Madrid

Alkali: Sandro Schaerer (Switzerland)

Wuri: Celtic Park

Lokaci: 8:00 na Yamma

RB Leipzig da Shakhtar Donestk

Alkali: Joao Pinheiro (Portugal)

Wuri: Red Bull Arena Leipzig

Lokaci: 8:00 na Yamma

(Rukunin G)

Borussia Dortmund da FC Copenhagen

Alkali: Francois Letexier (Faransa)

Wuri: Signal Iduna Park

Lokaci: 5:30 na Yamma

Sevilla da Manchester City

Alkali: Davide Massa (Italiya)

Wuri: Estadio R. Sanchez Pizjuan

Lokaci: 8:00 na Yamma

(Rukunin H)

Benfica da Maccabi Haifa

Alkali: Andreas Ekberg (Sweden)

Alkali: Estadio da Luz

Lokaci: 8:00 na Yamma

Paris Saint Germain da Juventus

Alkali: Anthony Taylor (Ingila)

Wuri: Parc des Princes

Lokaci: 8:00 na Yamma