✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wasiyyar marigayi Sheikh Ja’afar ga matasa lokacin siyasa

Ya gabatar da hudubar ne kwana daya kafin a kashe shi

Wannan wasiyya ta marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam (Rahimahullah) ya gabatar da ita ce a ranar Alhamis 25 ga Rabi’ul Auwal, 1428, daidai da 12 ga Afrilun 2007 wato a daren Juma’ar da aka kashe shi, kwana daya kafin ya jagoranci Sallar Asuba a Masallacin Juma’a na Almuntada da ke dorayi a Kano.

An shirya wani taron lacca ne a Masallacin Juma’a na Usman Bin Affan da ke kofar Gadon kaya, kai-tsaye ya zo wajen laccar daga dawowarsa daga Bauchi.

Ita wannan lacca malamai uku ne suka gabatar da ita, wato Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo da Malam Aminu Ibrahim Daurawa da Sheikh Muhammad Nazeefi Inuwa. Kuma kasancewar Sheikh Ja’afar ya dawo daga tafiya sai aka ba shi minti 10 ya yi ta’aliki a kai.

Ga yadda ta’alikin nasa ya kasance: Bayan godiya ga Allah, tare da yin salati ga Manzon Allah (Salallahu Alaihi Wasallam), sai ya ce “Ya ’yan uwa Musulmi! Abin da zan fada a nasihata ta karshe,” Allahu Akbar wannan jumla ita Malam Ja’afar ya bude maganarsa da ita, kamar ya san washegari Juma’a zai riga mu gidan gaskiya. Sai ya ci gaba da cewa “Mu ji tsoron Allah mu duka, da za mu yi zabe.”

Wato ya yi wannan nasiha ce ana jajiberin zaben gwamnoni da ’yan majalisar jihohi na shekarar 2007. Sannan ya ci gaba da cewa. “Asalin zaben nan malamai sun yi bayaninsa, duk mutumin da za ka zaba, ya zama cewa za ka zabe shi ne ba don maslahar kanka ba kai kadai, sai don maslahar al’umma gaba daya. Akwai mutanen da suke fama da kuncin tunani, wadanda tunaninsu me za su samu a karkashin dan takara, sannan su ce a zabe shi; ko me suka rasa, da za su ce kada a zabe shi.

In da dan takara zai zo ya ba ni Naira miliyan 10 ni kadai a matsayina na Ja’afar amma ya ha’inci al’ummar da yake wa mulki ta hanyar sauran bukatunsu, wadanda a asusun gwamnati akwai kudaden da za a iya yin wadannan bukatu na al’umma, amma yaki yi, ni kuma in kalli miliyan goman nan in ce ku zabe shi.

To, alal hakika na ci amanar kaina, kuma na ci amanar ku talakawa bayin Allah. Shi kuma shugaba na ha’ince shi. In da shugaba zai hana ni ko kwabo, amma ya zamo kudaden da ya karba daga asusun Gwamnatin Tarayya ya aiwatar da su ta hanyar da ta dace. To wajibina ne, in kiraye ku cewa ku zabe shi. Ba a dauki ma’aunin na ni me na samu ko me na rasa ba, masu irin wannan su ne wadanda suka jahilci addini kuma suka jahilci rayuwa.

Domin wannan shi ne ya kai Najeriya cikin halin ka-ka-ni-ka-yi. Ganin in amfana ni kadai ko kuma a bude mana wata kafa mu ’yan tsiraru shi ke nan sai mu yi shiru alhali mun san abin da shugaba yake yi ha’inci ne, amma sai mu daure masa gindi, hasali ma mu dinga kururuta cewa dole ne jama’a su zabe shi, ba don komai ba sai don abin da bai taka kara ya karya ba.

To wannan kuntataccen tunani ne, kuma rashin hangen nesa ne, rashin sanin ya kamata ne. Kullum za ka kalli me muka samu na ci gaba, ba me ni kadai na samu ba.” Allahu Akbar sai Malam ya kara da cewa “Ina kira ga ku matasa ku lura da yadda ake amfani da ku.”

Malam ya buga wani misalin abin da ya gani yayin da yake dawowa daga tafiya sai ya ce “dazu na shigo Kano dab da lokacin Sallar Magriba kafin zuwana nan sai na ga wadanda suke kamfen wato da alamu an yi yawo da su cikin gari ne za su koma gida. Na ga yara matasa an ciko su a kan a-kor-kura su kusan hamsin a cikin motar nan kai da ganinsu babu wanda ya yi Sallar Azahar ballantana La’asar kuma galibinsu da alamu sun bugu mota tana ta layi da su suna ihu suna dauke da hotuna suna sai wane! Sai wane! Kuma su wadanda suke ba da kudi a yi hakan ciki babu ’ya’yan su, nasu suna can, sun kai su mayan makarantu na cikin gida ko na waje.

Wannan shi ne hakakanin cin amanar al’umma, kai wannan shi ne hakikanin rashin mutunci, ka haukata ’ya’yan talakawa bayan ka yunwatar da su, kuma ka jahiltar da su babu ilimin addini babu na rayuwa, su kashe lokaci mai tsawo suna dauke da hotunanka, kan kana son ka tsaya zabe a wani mataki.

A kan abin da za a ba su wanda bai gaza Naira 300 ko 350 ba (a lokacin).” Sannan Malam ya ci gaba da nanata maganarsa ta farko inda ya ce “Hakika wannan ya kamata a yi hattara, duk wanda za mu zaba, kada mu kalli me ya ba mu, mu kalli dacewarsa da cancantarsa.

Duk wanda za mu zaba ya kasance ya cancanta ko ya ba mu kudi ko bai ba mu ba. Duk wanda bai cancanta ba to ko ya ba mu Fam taba sama, to, mu kada shi wannan shi ne gaskiyar lamari, amma idan kuka tsaya da jahilci da kuntatacciyar kwakwalwa, ta an ba ni kaza ni na ci kaza.

To wannan tunani na ci baya ne ba tunani ne na wanda ya san abin da ya kamata ba.” Sai Malam ya kara da cewa “Abin haushi da takaici hatta wadansu masu magana da yawun addini akwai masu irin wannan kuntataccen tunani, Ubangiji Ta’ala Ya yi mana gam-da-katar.”

A nan Malam yana magana ce a kan irin malaman da suka shiga siyasa tsundum da sunan malanta, suna taya wasu ’yan siyasa kamfen don watakila alakar da suke da ita, ko kuma don an ba su wani dan abin hasafi wanda yanzu ’yan siyasa ke bin malamai gida-gida suna ba su abin batarwa. Allahu Akbar! Wannan ita ce wasiyyar da Malam ya yi ta karshe ga matasa da duk wani mutum mai hankali.

Bayan an kammala wannan muhadara da niyyar washegari Juma’a Malam zai yi huduba a kan zabe.

Ranar Juma’a da Asuba Malam Ja’afar yana cikin Sallah, ya karanta Suratul Ma’arij aka samu wasu miyagun mutane azzalumai makiya Allah makiya san ci gaban addini, suka harbe shi da bindiga ba sau daya ba, ba sau biyu ba, inda suka harbe shi a kirjinsa gefen hagu, kuma wannan harbi ne ya yi sanadiyar rasuwarsa a wannan rana.

A nan muna rokon Allah Ta’ala ya sa Malam Ja’afar ya yi shahada kuma Ya karbi shahadarsa, Ya kyautata bayansa, Ya sanya albarka a cikin iyalansa da zuriyarsa.

Wadanda suka aikata wannan aiki na ta’addanci a kansa, su sani wannan gida da Malam Ja’afar ya tafi, kowane mahaluki sai ya je, ma’ana dukkanmu da muke raye yanzu watan wata rana za mu mutu mu tarar da shi baki dayanmu. A nan fatarmu ita ce ’yan uwa matasa a natsu a hankalta dangane da batun wannan zabe, musamman nan da a karshen wata jam’iyyun siyasa za su fara yakin neman zabe.

Don haka, kada matasa su bari a yi amfani da su ta hanyoyin da ba su kamata ba, a guji jefa kai a cikin abubuwan da ba za su haifar da da mai ido ba. Sannan burinmu a ce an yi tsaftataccen yakin neman zabe ba tare da amfani da makamai ko abubuwan da za su kai ga zubar da jini ba.