✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WASSCE: Dalibi mai COVID-19 zai rubuta jarabawa a makaranta

Wani dalibi daga cikin mutanen da aka killace saboda kamuwa da cutar COVID-19 zai rubuta jarabawar kammala sakandare (WASSCE) a farfajiyar makarantarsu. Zuwa yanzu babu…

Wani dalibi daga cikin mutanen da aka killace saboda kamuwa da cutar COVID-19 zai rubuta jarabawar kammala sakandare (WASSCE) a farfajiyar makarantarsu.

Zuwa yanzu babu cikakken bayani kan yadda zai rubuta jarabawar; na ko zai rubuta a ware ne, ko kuma tare da sauran dalibai.

A shafin Twitter na Hukumar Kula da Lafiyar Al’umma da Bayar da Taimakon Gaggawa ta Gombe, @GombePHEOC, an dauko dalibin ne daga inda aka ware wa masu fama da cutar cikin mortar daukar marasa lafiya.

Zai rubuta jarabawarsa ne ta biyu ta gwajin sinadarai (Chemistry practical) a makarantar sakandare ta kimiya da ke garin Gombe, (GSSS, Gombe).

An ce kuma za a kai shi ne dakin gwajin sinadarai na makarantar.