✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu daga cikin manyan sarautu da Masarautar Zazzau ta aro daga Borno

Masarautar Zazzau tana daya daga cikin fitattun masarautu a Najeriya. A wannan mako mun ciro wani rubutu ne da Sarkin Ayyukan Zazzau Alhaji Abbas Mohammed…

Masarautar Zazzau tana daya daga cikin fitattun masarautu a Najeriya. A wannan mako mun ciro wani rubutu ne da Sarkin Ayyukan Zazzau Alhaji Abbas Mohammed Fagachi ya yi a shafin “Kasar Zazzau a Jiya Da Yau”  wanda aka sanya a ranar 10 ga Satumban 2019, kan wasu sarautu da masarautar ta aro daga tsohuwar Daular Borno. A sha karatu lafiya:

Manyan sarautu da Masarautar Zazzau ta aro daga Daular Borno tun lokacin mulkin Habe kafin Jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo har zuwa yau su ne.

  1. Waziri: Sarautar Waziri ta samo asali ne daga Borno, kuma kalma ce da aka samo daga harshen Larabci wadda take nufin Mataimaki. Wannan sarauta an fara ta a Zazzau tun kafin zuwan daular Fulani.
  2. Arjinoma (Magajin Malam): Sarautar Arjinoma ita ce ta koma sarautar Magajin Malam, Arjinoma sarauta ce a cikin kalmar Barbarci wadda Hausawan Zariya suka canja mata suna zuwa Magajin Malam sakamakon zama da Wakilin Shehun Borno ya yi a Zariya a lokacin da aka rasa daya daga cikin Magajin Gidan Kona, ta nan ne aka samu wannan suna na Magajin Malam har ta zama sarauta a Zazzau.
  3. Galadima: Wannan sarauta ta Galadima tana daya daga cikin manyan sarautun Barebari kuma daya daga cikin ’yan Majalisar Shehun Borno, wanda kusan duk masarautun kasar Hausa ba inda babu ita. Wannan sarauta ta Galadima an fara nada ta tun a lokacin mulkin Habe a kasar Zazzau, haka kuma a Zazzau Galadima yana daya daga cikin ’yan Majalisar Sarki.
  4. Zarma (Bakon Borno): Wannan sarautar tana daya daga cikin manyan sarautu a Zazzau tun lokacin mulkin Habe, wadda ita ma Hausawan Zariya suka canja mata suna daga Zarma zuwa Bakon Borno sakamakon zuwan da yake yi shekara-shekara daga Borno a matsayin dan aike a tsakanin Shehun Borno da Zazzau domin karbar kudin kasa bisa umarnin Shehun Borno kamar yadda wadansu masana tarihi suka fada. Ita wannan sarauta an dade ba a nada ta ba tun bayan zamanin mulkin Sarkin Zazzau Malam Aliyu Dan Sidi, gidansa na Zariya a tsakanin Kanfage zuwa Unguwar Sarkin Magina.
  5. Kaigama: Sarautar Kaigama tana daya daga cikin manyan sarautu a Zazzau wadda aka fara ta tun lokacin mulkin Habe a Zazzau, kuma tana daya daga cikin sarautun da suka samo asali daga Borno kuma shi ne Shugaban Rundunar Mayakan Shehun Borno.
  6. Shettima: Sarautar Shettima tana daya daga cikin sarautun da kasar Zazzau ta samu daga Borno tun lokacin mulkin Habe har zuwa yanzu da Fulani suke mulki.
  7. Ciroma: Sarautar Ciroma ita ce sarautar da ta fi girma a cikin sarautun ’ya’yan Shehun Borno, kuma ba a ba kowa sai dan Shehu na cikinsa a wancan lokaci, amma yanzu an samu canje-canje. Wannan sarauta an fara nada ta ce a Zazzau ne lokacin mulkin Sarkin Zazzau Malam Jafaru Dan Isiyaku, wanda aka fara nadawa shi ne Malam Muhammadu Aminu daga gidan Sarautar Mallawa.
  8. Yerima: Sarautar Yerima tana daya daga cikin manyan sarautu na ’ya’yan Sarki a Borno kuma yana da yanki da yake dubawa a matsayin wakilin Shehun Borno, ana kiran yankin da suna Yankin Yeri. Wannan sarauta an fara nada ta a Zazzau a wannan lokaci na mulkin Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, wanda aka fara nadawa shi ne Malam Munir Jafaru dan Sarkin Zazzau Malam Jafaru.

8.Talba: Ma’anar kalmar sarautar Talba da Barbarci ita ce Alkali mai hukuncin miyagun laifuffuka. Wannan sarauta an fara nada ta a Zazzau cikin lokacin mulkin Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, wanda aka fara nadawa shi ne Alhaji Abdulkarim Aminu (Wamban Zazzau) dan Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu.

  1. Maina: Sarautar Maina na daya daga cikin sarautun Barebari, ita wannan sarauta ma’anarta duk wani dan Shehun Borno ko dan dan uwa ko dan tsohon gidan Sarautar Borno to sarautarsa Maina. An fara nada wannan sarauta a Zazzau cikin wannan zamani na Sarkin Zazzau Alhaji Shehu idris.
  2. Kachalla: Sarautar Kachallah tana daya daga cikin sarautun da ke da matsayi a Borno shi ne daya daga cikin ’yan kai sakon Shehun Borno a kasashen Hausa, wanda kuma a kasar Zazzau tana cikin manyan sarautu tun lokacin mulkin Habe zuwa yau.
  3. Bulama: Ma’anar sarautar Bulama shugaban al’umma basaraken da jama’a ke karkashinsa. Wannan sarauta tana daya daga cikin sarautun da aka aro daga Borno cikin wannan lokaci na mulkin Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, wanda aka fara nadawa shi ne Alhaji Shamsuddeen M.D Yusuf.