✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna 3 sun kubuta

Fasinjojin uku sun kubuta bayan wani bidiyo mai tayar da hankali ya karade kafafen watsa labarai.

Wasu mutum uku daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, sun kubuta sa’o’i 24 bayan da ‘yan ta’addan da suka sace su, sun fitar da wani hoton bidiyo mai tayar da hankali suna azabtar da su.

Aminiya ta tabbatar da kubutar mace daya da maza biyu wanda suka sake haduwa da ‘yan uwansu.

Ba a bayyana ko an biya kudin fansa kafin a sakimsu ba.

Wani mawallafi mazaunin Kaduna, Tukur Mamu ya tabbatar da sakin su ga Aminiya.

“Eh uku daga cikin wadanda abun ya rutsa da su sun kubuta, an saki mace daya da maza biyu. Amma ka sani ban shiga tsakani don sakinsu ba.” A cewarsa.

Idan dai za a iya tunawa Mamu ya fice daga shiga tsakani don yin sulhu sakamakon barazana da ake yi wa rayuwarsa.

A ranar Lahadi ne ‘yan ta’addan fa suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, suka saki wani bidiyo da ya nuna yadda suke azabtar da fasinjojin.

Sai dai bidiyon ya yamutsa hazo, inda mutane da dama ke ganin gwamnatin tarayya ta gaza yin wani abu don ceto fasinjojin.