✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu karin mutum 1,355 sun kamu da coronavirus a Najeriya

Adadin wadanda suka sake kamuwa da cutar ya sake karuwa a ranar Laraba.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), ta ce an samu karin mutum 1,355 da suka kamu da cutar coronavirus a ranar Laraba a fadin Najeriya.

NCDC ta sanar da samun karin masu cutar ne ta shafinta na intanet a daren ranar Laraba.

Jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan sabbin masu cutar da mutum 1,036, sai Nasarawa da 92, Delta mutum 58, Abuja 57, sannan Edo mutum 44.

A Jihar Ribas kuma mutum 25 ne suka kamu, Kano mutum 23, Enugu 11, Filato mutum bakwai, sai Jihar Bayelsa da aka samu mutum uku.

Kawo yanzu, adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan bullarta ya kai 240,374, wadanda daga cikinsu aka sallami mutum 213,491 daga cibiyoyin killace masu cutar.

Daga cikin masu cutar, adadin wadanda suka rasa rayukansu a fadin Najeriya ya kai 3,028.

NCDC ta jadadda muhimmancin bin matakan kariyar COVID-19, yin gwajin cutar da kuma karbar allurar rigakafin cutar.