✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu manyan abubuwan da suka faru a fagen siyasa a bana

A shekarar nan an samu dambarwar siyasa a manyan jam’iyyun kasar nan biyu.

Shekara kwana inji masu iya magana, kamar yau muka shiga bana, sai ga shi nan da mako daya za mu yi ban-kwana da shekarar.

Aminiya ta yi waiwaye kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi siyasa a shekara mai karewa.

A shekarar nan an samu dambarwar siyasa a manyan jam’iyyun kasar nan biyu daga ciki akwai:

Zaben Gwamnan Jihar Anambra:

Zaben Gwamnan Jihar Anambra, zabe ne da ya zo a daidai lokacin da jihohin Kudu maso Gabas suke fama da tashe-tashen hankali da ’ya’yan Kungiyar IPOB mai son kafa kasar Biyafara suke haddasawa.

’Ya’yan IPOB sun yi barazanar ba za a yi zaben ba, amma saura kwanaki kadan suka janye barazanar a daidai lokacin da gwamnati ta tura dimbin jami’an tsaro don tabbatar da ganin an yi zaben.

A karshe dan takarar Jam’iyyar APGA mai mulkin jihar Farfesa Charle Soludo ne ya lashe zaben.

Zaben shugabannin APC da PDP a jihohi da shiyyoyi

Jam’iyyar APC ta gudanar da zaben shugabanninta a matakan unguwanni da kananan hukumomi da jihohi, zabubbukan da suka a bar baya da kura a mafi yawan jihohin.

A jihohi irin su Kano da Kwara da Sakkwato jam’iyyar ta dare gida biyu, inda a Kano aka samu tsagin Malam Ibrahim Shekarau ya fitar da Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a matsayin shugaban jam’iyyar, shi kuma tsagin Gwamna Ganduje ya sake zabar Alhaji Abdullahi Abbas.

Wata kotun tarayya a Abuja ta tabbatar da Alhaji Haruna Zago a matsayin shugaba, yayin da bangaren Gwamna Ganduje ke shirin daukaka kara.

Haka a Kano, Jam’iyyar PDP ma ta hadu da tata matsalar inda aka samu rashin jituwa a kan wane tsagi ne zai fitar da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Shiyyar Arewa maso Yamma, inda aka yi ta samun sa-in-sa a tsakanin bangaren Sanata Kwankwaso da na Alhaji Aminu Wali, hakan ya sa dole jam’iyyar ta dage taron shiyyar Arewa maso Yamma.

Rusa Shugabancin Secodus a PDP

A shekarar mai wucewa ce aka yi ta takaddama a kan shugabancin Jam’iyyar PDP inda jiga-jigan jam’iyyar suka nemi Shugaban Jam’iyyar na Kasa Yarima Uche Secondus ya sauka daga mukaminsa, shi kuma ya kekasa kasa ya ce babu wanda ya isa ya sauke shi daga kan kujerarsa.

Bayan zuwa kotu da kuma yadda wadansu matasa suka mamaye Sakatariyar Jam’iyyar ta Kasa suna neman Secondus ya sauka, a ranar 30 ga Oktoba, jam’iyyar ta gudanar da zaben shugabanninta, inda ta zabi Sanata Iyorchia Ayu a matsayin shugabanta na kasa ta hanyar sasanci.

Zaben da ake ganin nasara ce ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar wanda Ayu ya fito daga bangarensa.

Tilas a mika mulki ga Kudu – Gwamnonin Kudu

Wata takaddama da ta taso a fagen siyasa ita ce matsayar da Kungiyar Gwamnonin Kudu ta cimma cewa dole ne Shugaban Kasa na gaba ya fito daga yankinsu.

Kungiyar ta yanke shawarar ce a taron da ta yi a Legas, inda Shugaban Kungiyar Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya ce, suna goyon kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Amma ta ce dole Shugaban Kasa na gaba ya fito daga yankinsu, kuma a bi tsarin karba-karba a tsakanin Arewa da Kudu,. Gwamnonin kuma sun amince da wasu bukatu da suke son a aiwatar da suka shafi tsaro da yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da kuma dokar man fetur.

Matsayar gwamnonin Kudun ta samu goyon baya daga wadansu ’yan siyasa daga Arewa ciki har da gwamnoni da sanatoci da sauransu.

Misali Sanata Muhammad Ali Ndume na Jam’iyyar APC ya nuna goyon bayansa ga kungiyar.

Masu irin wannan ra’ayi suna cewa yin haka shi ne adalci, tunda dan Arewa, ya samu wa’adin mulki biyu a karkashin jam’iyyar, don haka sake tsayar da dan takara daga Arewa zai zamanto tauye ’yan Kudu.

Kama Nnamdi Kanu da Igboho

A banar ce bayan gwamnatin Najeriya ta samu nasarar kamo Mista Nnamdi Kanu, mai rajin ballewa daga kasar nan domin kafar kasar Biyafara da aka ce an kamo shi ne daga kasar Kenya.

Kwanaki kadan kuma jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), suka kai samame gidan mai fafutikar kafa kasar Yarbawan nan Sunday Igboho, inda suka ce sun gano manyan makamai.

Shi kuma sai ya arce amma jamia’n tsaron Jamhuriyyar Benin suka kama shi, inda yake tsare a can.

Tinubu ya soki sabunta rajistar mambobin APC

Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar 9 ga Fabrairun bana ya soki aikin sake rajistar ’ya’yan Jam’iyyar APC da aka fara, inda hakan ya tayar da kura a jam’iyyar.

Tinubu wanda ake kyautata zaton zai nemi tsayawa takarar Shugaban Kasa a zaben 2023, ya ce aikin sabunta rijistar ’ya’yan jam’iyyar da ke gudana ba ya da wani tasiri.

“Sabunta rijistar da jam’iyyar ke yi tamkar a sanya daya ne kana kuma a cire daya, don haka ni ina ganin ba wata ƙaruwa ba ce,’’ inji Tinubu.

Wannan kalami wata alama ce da ke nuna cewa bai ji dadin abin da ake yi ba, saboda a cewar masu fashin baki yana ganin, aikin rajistar zai iya rage masa karfin mamayar da ya yi wa jam’iyyar, da kuma tasirin da yake da shi a cikinta.

Canja shekar gwamnonin PDP zuwa APC A ranar 27 ga Yunin bana Jam’iyyar APC ta yi babban kamu inda Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle ya koma jam’iyyar daga PDP.

Sai dai Mataimakinsa Mahdi Aliyu yaki bin sa.

Wannan wani ci gaba ne da APC ta samu, sai dai canja shekar tasa ta jawo ce-ce-ku-ce a jam’iyyar, bayan da Shugaban Riko na Jam’iyyar na Kasa Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana shi a matsayin jagoran jam’iyyar a Jihar Zamfara, wannan lamari ya ta da kura sosai a tsakaninsa da tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Abdul’azeez Yari.

Shi ma Gwamna Jihar Kuros Riba Ben Ayade ya sauya sheka zuwa APC a banar. Ayade ya bayyana komawarsa APC ne bayan ya karbi bakuncin wadansu gwamnonin APC 7 a karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni.

Sannan a ranar 17 ga Satumba sanannen mai sukar Shugaba Buhari, Mista Femi Fani Kayode ya koma Jam’iyyar APC, bayan shafe kusan wata bakwai ana yamadidin cewa zai koma jam’iyyar.

Yoyon ruwan sama a Majalisar Dokoki ta Kasa

A ranar 22 ga Yunin bana ne ruwan sama ya rika zuba a harabar Majalisar Dokoki ta Kasa. Rahotanni sun ce rufin ginin majalisarya fara yoyo ne lokacin da aka yi wani ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Cibiyar ’yan jarida masu dauko rahotanni daga majalisar ma bai tsira daga yoyon ruwan ba.

Hakan ya sa ma’aikata masu kula da tsabtace majalisar suka yi ta faman kwashe ruwan inda sai da suka shafe fiye da minti 20 wajen kwashe ruwan.

Zabe ta na’ura

A Oktoban bana ne Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince Hukumar INEC ta aika sakamakon zabe ta Intanet bayan ta amince hukumar ta yi amfani da na’ura domin aika sakamakon zabe.

Majalisar ta sauya ra’ayi ne bayan da farko ta ki amincewa da tura sakamakon zabe daga muzabu ta Intanet.

Takkadama kan Dokar Zabe

Daya daga cikin manyan abubuwan da suka jawo hankali a harkokin siyasa a bana, shi ne batun Dokar Zabe da aka gyara, wadda har yanzu ake ta ce-ceku-ce a kan sa hannu a kanta.

Babban bangaren dokar da ya fi jawo takaddama shi ne na kyale dukkan ’ya’yan jam’iyya su zabi ’yan takara maimakon wakilan jam’iyya.

A kan haka ne Shugaban Kasa ya ki sa wa dokar hannu, inda yanzu haka Sanatoci suka fara karbar sunaye domin jefa kuri’ar tilasta aiki da dokar.