✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ruwa ya ci matasa ’yan makaranta 2 a Zariya 

Matasan sun bace a kogin bayan da suka je wanka.

Wasu matasa biyu, ’yan aji daya a karamar Sakandaren Gwamnati da ke Zariya a Jihar Kaduna, sun nitse a ruwa a lokacin da suke ninkaya a Kogi.

Matasan da suka gamu da ajalin nasu sune Zakariya Aliyu Yahaya da Yusuf Abdullahi, masu shekaru 17 da 16.

Wani abokinsu mai suna Musa Dogara ne ya bayyana rasuwar matasan a Angwar Sirdi a Zariya, inda ya c, “Bayan faduwar rana ne ba su dawo ba, sai muka fara nemansu, nan take wani abokinsu ya sanar da mu cewa sun tafi wanka kogi.”

Iyayensu sun bayyana cewar tun da sun fara yin hankalin kansu, ba su damu da inda suka shiga ba sai dai aka kwana daya ba tare da an ji duriyarsu ba sannan aka shiga nemansu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige bai tabbatar da faruwar lamarin ba.

Amma ya ce za su bincika da zarar sun samu wani bayani, za su yi wa manema labarai karin haske.