✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata 74 rabon da a biya mu hakkokinmu —’Yan fanshon Binuwai

’Yan fansho sun yi zanga-zanga kan wata 74 da ba tare da biyan su hakkokinsu ba a Jihar Binuwai.

’Yan fansho sun yi zanga-zanga kan wata 74 da aka shafe ba tare da biyan su hakkokinsu ba a Jihar Binuwai.

’Yan fanshon da suka yi ritaya daga aikin gwamnatin jihar sun zargi gwamnatin Gwamna Ortom da biyan wasusnu Naira 800 a wata, maimakon hakkokinsu da suka kamata.

Sun bayyana cewa baya ga masu bin jihar hakkokinsu na wata 74, akwai masu bin na wata 37, baya ga kudadensu na garatuti na shekaru takwas da gwamnatin ta yi watsi da shi.

Jagoran zanga-zangar, karkashin inuwar Concerned Aggrieved Pensioners, Akosu Ioream, ya  ce, “Sakamakon haka, ’yan fansho na ta mutuna, saboda rashin kudin abinci da magunguna ga masu larura.

“Hakan ya sa mun rasa iyalanmu, tunda ba mu da karfin daukar dawainiyarsu, ga cututtukan tsufa, ga kuma yunwa,” in ji shi.

Don haka suka yi tattaki zuwa Majalisar Dokokin jihar domin bayyana ransu da kuma neman mafita.

Da yake jawabi a madadin Shugaban Majalisar, Oliver Aguda, ya ce shugaban majalisar wanda yanzu ke takarar gwamnan jihar karkashin Jam’iyyar PDP ba ya gari, amma zai isar da sakonsu gare shi.

’Yan fanshon sun sake zanga-zanga a karo na uku ranar Laraba, inda suka yi wa gidan gwamnatin jihar tsinke, don neman biyan su kudin garatutinsu na shekaru takwas.

Shugaban kungiyar tsoffin ma’aikatan, Steven Daniel Zitta, ya shaida wa ’yan jarida cewa, ’ya’yan kungiyar na ta mutuwa ba tare da sun karbi hakkokin nasu ba.

Ya ce da dama daga cikinsu sun gamu da larurorin hawan jini da mutuwar bakin jiki, wasu kuma sun mutu, saboda halin da suka shiga na rashi.

Sun kuma ce duk lokacin da suka yi zanga-zangar zuwa gidan gwamnati, sai a ce musu gwamnan ya yi tafiya.

Sun kuma zargi kungiyar ’yan fansho ta kasa da yin biris da halin da suke ciki.

Sai dai mataimakin gwamnan jihar, Ahmad Muhammad Ketao, ya ce gwamnatin za ta duba kokensu, tare da sanya musu ranar Alhamis domin tattaunawa da su a hukumance.