✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata bakwai an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

Irin hakan ne ya shafe mu har ya jawo a shekarar 2019 muka fadi zabe.

Idan za a tuna, zaben shugabannin Jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma an dakatar da shi bayan rikicin da bangaren tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da na tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Aminu Wali suka fara a kan mukamin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar a Shiyyar Arewa maso Yamma.

Aminiya ta ruwaito cewa, mukamin wanda aka bayyana cewa dan Jihar Kano ne zai samu, ya ta da kura a tsakanin bangarorin biyu masu fatar rike mukamin domin kara musu haske a shekarar 2023.

Mukamai 17 na yankuna sun hada da manyan mukamai 7 wadanda za a rarraba a tsakanin jihohin yankin bakwai.

Majiyar Aminiya ta ce rikicin ya samo asali ne a taron da Jam’iyyar PDP ta gudanar a Kaduna inda aka samu musayar yawu a tsakanin bangaren Sanata Rabi’u Kwankwaso da na Aminu Wali a kan wanda zai haye kujerar Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na shiyyar.

Wannan mukami na Matamakin Shugaban Jam’iyyar da aka damka shi ga Jihar Kano, lamarin ya janyo wani karamin yaki a tsakanin bangarorin biyu don samun mukamin wanda zai iya zama hanya ko mabudi na samun dama a zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Mukamai 17 da aka ware wa yankin Arewa maso Yamma tuni sun raba su a tsakanin jihohin da ke yankin da suka hada da Kano da Kaduna da Jigawa da Katsina da Sakkwato, da Kebbi da Zamfara.

A lokacin da aka yi wancan taron a ranar 10 ga Afrilun bana a Kasuwar Baje-Koli ta Jihar Kaduna an samu ba-takashi a tsakanin magoya bayan tsohon Gwamna Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma na Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal lamarin da ya janyo aka dage taron.

Sanata Kwankwaso ya zargi Gwamna Tambuwal da goyon bayan Aminu Wali tare da shiga harkar siyasar Jihar Kano zargin da Gwamna Tambuwal ya musanta tare da ambatonsa a matsayin zargin da ba ya da “tushe.”

Wannan lamari dai shi ya tilasta Shugaban Jam’iyyar PDP ya kafa kwamitin riko a shiyyar.

Kwankwaso da Ambasada Nuhu Wali

Rigimar Sanata Kwankwaso da Ambasada Wali ta samo asali ne tun a shekarar 2018 lokacin da Kwankwaso ya dawo Jam’iyyar PDP inda kuma uwar jam’iyyar ta kasa ta ba shi kashi 51 na mukaman jam’iyyar yayin da aka bar sauran kashi 49 ga sauran manyan jam’iyyar wato Aminu Wali da Malam Ibrahim Shekarau (kafin ya koma (APC) da kuma Bello Hayatu Gwarzo.

Mai magana da yawun Kwankwasiyya kuma jigo a tafiyar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya shaida wa Aminiya cewa bayan da wadancan riginginmu suka faru a Kaduna, a daidai lokacin da Kwankwaso ya goyi bayan sulhun da za a yi tsakaninsa da Gwamna Tambuwal sai ya fahimci cewa akwai kullalliya a tsakanin Ambasada Wali da Gwamna Tambuwal.

Ya ce da a ce shugabanin jam’iyyar irin su Wali da Tambuwal ba su hadu sun nemi tsayar da Mohammed Jamo a matsayin halattaccen Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ba, to, da tun farko rigingimun su faru ba.

Haka kuma Kwankwaso ya zargi Gwamna Tambuwal da hada baki da Aminu Wali wajen daukar nauyin Sanata Bello Hayatu Gwarzo a kan neman wannan mukami, duk da cewa ya san Aminu Wali da Hayatu Gwarzo suna goyon bayan Jam’iyyar APC a Jihar Kano.

“Gwamnatin Kano kuwa ta saka musu da mukamin Kwamishinan Ruwa da Albarkatun Kasa inda Aminu Wali ya bayar da mukamin ga dansa na cikinsa wanda kuma ya taba yin takarar zaben fid-da-gwani na Gwamna a shekarar 2019,” inji shi.

A cewarsa bangaren Kwankwaso ba za su iya nade hannun su zuba ido suna kallo wadansu mutane na bangaren Wali suna cin zarafinsu ba.

Sai dai wani kusa a tafiyar gidan Aminu Wali, Alhaji Bako Lamido ya musanta batun cewa kafin gudanar da taron an samu hadin baki a tsakanin bangaren Aminu Wali da na Gwamna Tambuwal a kan fitar da wanda zai samu wannan mukami.

“Mu ne halattattun ’ya’yan Jam’iyyar PDP domin ba mu taba barin wannan jam’iyya ba. A shekarar 2014 lokacin da Kwankwaso yake Gwamnan Kano ya nemi mu bar jam’iyyar don komawa APC, amma muka ki yarda muka ci gaba da zama a jam’iyyar ta PDP.

“Wannan shi ne ainihin farkon matsala a tsakaninmu. Shi Kwankwaso yana tunanin cewa mun butulce masa saboda mun ce ba mu son komawa Jam’iyyar APC.

“Haka kuma a shekarar 2018 lokacin da Kwankwaso ya dawo PDP sai ya dauke mu a matsayin manyan makiyansa, inda ya ce ba za mu iya haduwa mu yi tafiya tare ba, duba da cewa a baya ya nemi mu yi tafiya tare muka ki amincewa,” inji shi.

A cewarsa sun tafi taron Kaduna ne da niyyar zaben Sanata Bello Hayatu Gwarzo wanda yana cikin ’yan gabagaban da suka kafa Jam’iyyar PDP tun a 1999 inda har ya yi Sanata a karkashinta.

Ya yi zargin cewa ’yan Kwankwasiyya ne suka kawo rikici a daidai lokacin da suka fahimci cewa dan takararsu Mohammed Jamo ba zai kai labari ba, sai suka tayar da hatsaniya.

“Sun san cewa idan an kammala zaben ba za su samu nasara ba sai suka tayar da rikici domin kowa ya rasa.

“Babu wata yarjejeniya da aka kulla a tsakanin bangaren Kwankwasiya da mu a kan amincewa da dan takara guda daya.

“ Mun san cewa za a gudanar da zabe wannan shi ne abin da aka cimma, kasancewar akwai mutane da yawa da suke neman wannan kujera,” inji shi.

Uwar Jam’iyya ta Kasa ta kafa kwamiti a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, lamarin da Kwankwaso ya ce ba ya adawa a kansa.

Sai dai kuma ta bayyana a fili cewa tsohon Gwamnan bai amsa gayyatar da kwamitin ya yi masa don sulhunta tsakaninsu da Aminu Wali ba.

Yayin da yake karin haske kan halin da ake ciki yanzu Shugaban Jam’iyyar, Alhaji Shehu Sagagi ya ce uwar jam’iyyar ta sanya ranar 9 ga Oktoba don yin taron, sai dai kuma hakan bai faru ba saboda ya zo daidai da lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara a Barikin Soji na Jaji da ke Jihar Kaduna “Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna ya ba mu shawarar mu dage taron.

Tun daga wancan lokaci sai aka ce za a gudanar da taron bayan an gudanar da Babban Taron Jam’iyya na Kasa, Wannan ne halin da ake ciki a yanzu.

Da yake karin haske kan abin da Sagagi ya fada Bako Lamido ya ce, “Shugabannin jam’iyyar na yanzu za su ci gaba da jan ragamar shugabancinta har zuwa ranar 9 ga Disamba, daidai lokacin cikar wa’adin mulkinsu inda za a rantsar da sababbin shugabanni da aka zaba.

“Na tabbata kafin wannan lokaci uwar jam’iyya za ta sa lokacin da za a gudanar da wannan zabe na shiyya,” inji shi.

Masu fashin bakin siyasa na ganin cewa idan ba a magance matsalar ba, to komai na iya faruwa wanda hakan zai iya shafar nasarar da Jam’iyyar PDP ka iya samu a zaben 2023.

“Irin hakan ne ya shafe mu har ya jawo a shekarar 2019 muka fadi zabe. Ina fata masu ruwa- da-tsaki za su tuna abin da ya faru da mu a shekarar 2019 ba za kuma su sake yarda hakan ta faru da mu ba.

“Ina da yakinin iyayen jam’iyyar da shugabanninta za su zo da wani abu da zai sa mu samu nasara a zaben shekarar 2023,” inji Bako Lamido.

Rikicin cikin gida da ya mamaye PDP ya hana ’ya’yanta su yi amfani da damar da rikicin gida da ke faruwa a jam’iyya mai mulki ta APC a Jihar Kano.

Rikicin da ke faruwa a Jam’iyyar APC shi ne yadda tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya jagoranci wata tafiya ta mutum bakwai da ake kira da G7 don kalubalantar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, hakan ya jawo musayar kalaman girmamawa a tsakanin Sanata Rabi’u Kwankwaso da Sanata Ibrahim Shekarau da suka sa jama’ar jihar ganin kamar tsofaffin gwamnonin suna shirin hadewa ne don kalubalantar Gwamna Abdullahi Ganduje.

Sai dai kuma a wace jam’iyyar? Lokaci ne kadai zai bayyana haka, musamman ganin a baya-bayan nan Sanata Shekarau ya ce ba zai bar Jam’iyyar APC ba.